'Yan Sanda Sun Sanya Dokar Takaita Zirga Zirga a Katsina, An Tsaurara Matakan Tsaro

'Yan Sanda Sun Sanya Dokar Takaita Zirga Zirga a Katsina, An Tsaurara Matakan Tsaro

  • A yayin da ake shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a Katsina, 'yan sanda sun takaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa
  • 'Yan sanda sun sanya dokar takaita zirga zirgar ne domin tabbatar da kare lafiyar masu zabe yayin gudanar da zaben ciyamomin
  • Hukumomin tsaro sun shirya dakile duk wata barazana kafin, a lokacin, da kuma bayan zaben tare da aika sako ga mazauna Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gabanin zaben ciyamomi na ranar Asabar a Katsina, rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar da takaita zirga-zirga daga karfe 6 na safe zuwa 4 na yamma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abubakar Sadiq, ya bayyana cewa an sanya dokar ne domin tabbatar da tsaro kafin, lokacin, da bayan zaben.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana da ta sanya dokar takaita zirga-zirga a jihar Katsina
'Yan sanda sun sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina ana dab da zaben ciyamomi. Hoto: @dikko_radda, @PoliceNG (X)
Asali: Twitter

'Yan sanda sun takaita zirga zirga a Katsina

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Jaridar Punch ta rahoto DSP Abubakar yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za a takaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa daga karfe 6 na safe zuwa 4 na yamma, a ranar Asabar, 15 ga Fabrairun 2025."

'Yan sanda sun dauki matakin ne domin tabbatar da tsaro da bada dama ga masu zabe su kada kuri’arsu ba tare da tsangwama ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Allyu Abubakar Musa, ya yi kira ga mazauna jihar da su bi dokar takaita zirga-zirgar domin tabbatar da zaman lafiya.

'Yan sandan Katsina sun shirya dakile barazana

Ya kara da cewa an samar da tsare-tsare na tsaro domin tabbatar da bin doka da kiyaye lafiyar masu zabe da jami’an zabe.

Kwamishinan ya yi kira ga masu zabe su fito kwansu da kwarkwatarsu, su yi amfani da damar kada kuri’a cikin lumana da bin doka.

Rundunar ta jaddada za ta dauki tsautstsauran mataki kan duk wani mutum ko kungiya da suka yi yunkurin karya doka ba tare da rangwame ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

Masu ruwa da tsaki sun roki jama’a su tabbatar da zaman lafiya tare da gujewa duk wata barna ko tashin hankali a lokacin zabe.

APC ta kaddamar da yakin zabe a Katsina

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya kaddamar da yakin neman zaben shugabannin ƙananan hukumomi a Katsina.

A taron, Ganduje ya karbi fiye da mutane 40,000 da suka sauya sheka zuwa APC, ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel