'Dan Majalisa Ya Gabatar da Kudurin Kirkirar Sababbin Jihohi 3, An Jero Sunayensu

'Dan Majalisa Ya Gabatar da Kudurin Kirkirar Sababbin Jihohi 3, An Jero Sunayensu

  • Dan majalisar wakilan tarayya, Hon. Oluwole Oke ya gabatar da kudurin sauya wasu sassa da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Kudurin da Hon. Oluwole ya gabatar ya nemi majalisar ta amince da kirkirar sababbin jihohi uku: Oke-Ogun, Ijebu da Ife-Ijesa
  • Haka kuma, majalisar ta saurari kudurin neman a yi bincike kan almundahana a ma’aikatar kudi da Ofishin Akanta Janar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta tattauna kan wasu muhimman kudurori da suka shafi jihohi, mulki da gudanarwar gwamnati.

Hon. Oluwole Oke, ya gabatar da kuduri gaban majalisar na son yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya (da aka sabunta) garambawul.

Majalisar wakilai ta tattauna kan wasu muhimman kudurori
Majalisar wakilai ta saurari kudurin neman kirkirar sababbin jihohi uku daga Hon. Oluwole Oke. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Dan majalisa yana so a kirkiri jihohi 3

'Dan majalisar wakilan, ya bukaci majalisar ta amince da kudurinsa na samar da karin sababbin jihohi uku, in ji rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Oluwole Oke wanda ya dauki nauyin kudirin da ke neman sauya sassa na kundin tsarin mulkin ya lissafa jihohin da yake so a kirkiro.

A cikin kudurin da ya gabatar, Hon. Oluwole ya nemi majalisar ta kirkiri jihohin Oke-Ogun, Ijebu da Ife-Ijesa.

Majalisa ta saurari muhimman kudurori

A jerin ayyukan ranar Alhamis, majalisar ta tattauna a kan kudurorin da ke jiran karatu na biyu.

Daga cikin kudurorin akwai kudirin kafa dokar kula da wasannin caca ta kasa, wanda mataimakin shugaban majalisar, Hon. Benjamin Kalu, ya dauki nauyinsa.

Kudirin zai rushe dokar wasannin cacar Lottery ta kasa, tare da neman samar da doka mai tsauri kan wasannin caca na yanar gizo.

Majalisar ta tattauna kan kudirin kafa kananan kotuna a babban birnin tarayya don yanke hukunci kan shari’o’in laifuffukan farar hula.

'Yan majalisa za su binciki ma'aikar kudi

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

Haka kuma, an duba kudiri na musamman na gyara dokar asusun raya noma ta 2022, domin bunkasa harkokin noma da inganta tallafi.

An gabatar da rahoton kwamitin hadin gwiwa kan hana fitar da masara daga kasar nan, wanda Hon. Babajimi Benson ya jagoranta.

Majalisar ta tattauna kan kudirin gyara sashe na 14(2) na dokar raya yankin Kudu maso Yamma don daidaitawa da manufofin kasa.

Haka kuma, an tattauna wani kudiri na binciken zargin almundahanar kudaden kwangila a ma’aikatar kudi da ofishin akanta janar., da dai sauran kudurorin.

An gabatar da bukatar kirkirar jihohi 31

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin majalisar wakilai mai duba kundin tsarin mulki ya ce an gabatar da bukatar kirkiro sababbin jihohi 31.

Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, ya karanta wasikar da ta yi bayanin sharuddan da ake bukata kafin amincewa da sababbin jihohin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.