An Kaddamar da Shirin Karban Tuban 'Yan Bindiga da Koya Musu Sana'o'i

An Kaddamar da Shirin Karban Tuban 'Yan Bindiga da Koya Musu Sana'o'i

  • Gwamnatin tarayya tare da goyon bayan gwamnatin Zamfara ta kaddamar da shirin na musamman kan 'yan bindiga da suka tuba
  • Rahotanni sun nuna cewa shirin zai bai wa 'yan bindigar da suka tuba damar samun horo na sana’o’i, sauya musu tunani da sauransu
  • A karkashin shirin, 'yan ta'addan da uka ki tuba za su fuskanci hare-haren soji da ake ci gaba da kaiwa kan 'yan bindiga a Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnatin tarayya tare da goyon bayan gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da shirin Operation Safe Corridor North West a jihar Zamfara.

Shiri na da nufin bai wa 'yan bindigar da suka yi nadama damar dawowa cikin al'umma ta hanyar sulhu, yin watsi da makamai, da kuma samun horo na sana’o’i.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi bayani a kan daidaita farashin abinci

Gwamnan Zamfara
An kaddamar da sabon shirin yaki da ta'addanci a Zamfara. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa yadda aka kaddamar da shirin a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dauki tsarin shirin daga irin wanda aka yi a yankin Arewa maso Gabas domin sauya tunanin tsofaffin mayakan Boko Haram da kuma sake shigar da su cikin al’umma.

A cewar hukumomi, shirin zai kasance wata hanya ta bai wa 'yan bindiga da suka tuba damar komawa rayuwa ta gari.

A halin yanzu, ana ci gaba da kai farmaki kan 'yan bindiga a Zamfara da makwabtanta, tare da tabbatar da cewa wadanda suka ki tuba za su fuskanci karfin dakarun sojin Najeriya.

Za a koyawa 'yan bindiga sana’o’i

Shirin Operation Safe Corridor North West zai bai wa wadanda suka ajiye makamansu damar samun horo a fannoni daban-daban.

Horon zai hada da koyon sana’o’i, karfafa tunaninsu ta hanyoyi daban daban da kuma gyara akidarsu domin kauce wa komawa ta’addanci.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

A cewar hukumomi, matakin zai taimaka wajen rage tasirin ‘yan bindiga a yankin, domin yana bai wa masu nadama wata mafita maimakon komawa ga laifuffuka.

Ana fatan cewa hakan zai taimaka wajen rage ta'addanci da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ke yi a Arewa ta Yamma.

Za a farmaki wadanda suka ki tuba

Duk da shirin gyaran halin, dakarun tsaro na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin 'yan bindiga a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Gwamnati ta ce za a hada dabaru na sulhu da na yaki domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

A cewar jami’an tsaro, duk wani da ya ki ajiye makamansa kuma ya ci gaba da aikata laifuffuka, zai fuskanci matakin soja ba tare da sassauci ba.

Shirin Operation Safe Corridor North West yana cikin matakan da gwamnati ke dauka domin dakile matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, wanda ya addabi al’umma.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram 129,000 sun tuba, ana ba 800 horo na musamman

An fatattaki 'yan fashi a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki kan wasu 'yan bindiga masu fashi da makami a Kaduna.

Bayan farmakin sojojin, 'yan fashin sun firgita sun tsere cikin daji kuma an ceto mutane biyu da 'yan ta'addar suka kama a kan hanya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng