Zargin Badakala: Kotu Ta Yi Zama a Shari'ar da Ake Tuhumar Ganduje da Matarsa

Zargin Badakala: Kotu Ta Yi Zama a Shari'ar da Ake Tuhumar Ganduje da Matarsa

  • Kotun Kano ta dage sauraron karar cin hanci da almundahana da ake tuhumar Abdullahi Ganduje da matarsa Hafsat Umar da wasu mutum shida
  • Gwamnatin Kano ta shigar da tuhume-tuhume takwas kan zargin cin hanci da almundahana da suka hada da karkatar da kudaden al'umma
  • Alkalin kotun, Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta amince da bukatun kara wa'adin lokacin gabatar da hujjojin kariya daga dukkan masu kare kansu
  • Hakan ya biyo bayan ci gaba da shari'ar da aka dade ana yi game da korafe-korafe kan tsohon gwamna, Ganduje da matarsa, Hafsat Umar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Babbar kotu a Kano ta saurari shari'ar da aka shigar kan tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje da kuma matarsa, Hafsat Umar da wasu mutane shida.

Kotu ta dage sauraron karar cin hanci da almundahana da ake yi wa Ganduje da wasu mutum bakwai har zuwa watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Kotu ta dage sauraran shari'ar da ake zargin Ganduje da matarsa
Kotu a Kano ta dage ci gaba da shari'a kan zargin Abdullahi Ganduje da badakala. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Twitter

Kotu ta saurari shari'ar Ganduje da gwamnati

Gwamnatin Kano ce ta shigar da kara kan zargin cin hanci, almundahana da karkatar da biliyoyin kudade kan Ganduje da matarsa Hafsat Umar, cewar Channels TV..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad da kamfanin Lamash da na Lasage General Enterprises Limited.

Lauyan gwamnati, Adeola Adedipe, SAN, ya bayyana a kotu cewa ya shirya ci gaba da sauraron karar tare da neman karin lokaci don daidaita wasu takardun kariya.

Ganduje: Wane mataki kotu ta ɗauka kan shari'ar?

Lauyan Ganduje da matarsa, Lydia Oluwakemi-Oyewo, ta bayyana cewa ta shirya ci gaba da sauraron karar, yayin da wasu lauyoyi suka nemi karin lokaci.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta amince da dukkan bukatun karin lokaci daga masu kare kansu tare da dage shari'ar zuwa Afrilu 15, 2025, Daily Nigerian ta ruwaito.

Dan APC ya fadi tasirin Tinubu a Kano

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta gano inda aka boye biliyoyin Naira na kudin harajin Kano

Kun ji cewa shugaban hukumar raya kogin Hadejia da Jama’are, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana yadda jihar Kano za ta yi ruwan kuri'a sosai ga APC.

Bichi ya soki gwamnatin Abba Yusuf ta NNPP, inda ya ce manufofinta sun sanya mutane sun daina sha'awar jam'iyyar tun kafin zabe.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kallon-kallo tsakanin yan APC da NNPP a Kano musamman kan zaben shekarar 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.