Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Matar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Matar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje

  • Hukumar yaki da rashawa EFCC ta cafke Hafsat Ganduje, matar gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta EFCC ta aike wa Hafsat Ganduje gayyata amma bata amsa ba
  • Abdulazeez Ganduje, dan Hafsat Ganduje ne ya shigar da korafi a kanta bisa zarginta da babakere kan kudin wasu filaye na wani mutum

Kano - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama, Haftsat Ganduje, matar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin rashaswa da rikicin fili da dan ta ya yi karar ta, Premium Times ta ruwaito.

An kama ta ne makonni bayan ta ki amsa gayyatar da hukumar ta EFCC ta yi mata.

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Matar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
Haftsat Ganduje, matar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Tunda farko dai EFCC ta gayyaci matar Gandujen zuwa hedkwatar ta a ranar 13 ga watan Satumba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Amma bata amsa gayyatar ba kuma EFCC ta yi barazanar kama ta. Majiyoyi na kusa da ita daga baya sun bayyana cewa ta tafi Birtaniya ne domin hallartar bikin kammala karatun danta.

Masu bincike na yi wa Haftsat Ganduje tambayoyi ne kan zargin da danta Abdulazeez Ganduje ya shigar a kanta.

Wani mutum da ke da masaniya kan kamen amma ya bukaci a sakaya sunansa ya ce an kama ta ne a 'yammacin ranar Litinin."

Hafsat Ganduje tana hedkwatar hukumar EFCC ana mata tambayoyi har zuwa karfe na safiyar ranar Litinin kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ta yaya matsalar ta fara?

Abdulazeez ne tafi wurin EFCC don yin korafi kan mahaifiyarsa Hafsat Ganduje a cewar wasu majiyoyi da ke kusa da iyalan bisa zargin ta da yin babakere kan wani fili da ya sayarwa wani.

Kara karanta wannan

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

Gwamna Ganduje kansa ya shiga matsala mai alaka da rashawa a 2018 yayin da jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke ikirarin Ganduje ne ke karbar rashawa daga hannun dan kwangila. Ganduje ya musanta hakan.

A cewar majiyoyi wadanda suka ga takardan korafin da Abdulazeez ya shigar, ya ce wani mai gini ya nemi ya taimaka shi samun filaye a Kano ya kuma bada dubban dalolin Amurka kimanin Naira miliyan 35 a matsayin kudin taimaka masa samun filin.

Premium Times ta ruwaito cewaa Abdulazeez ya saka kudaden a asusun ajiyar mahifiyarsa, Hafsat Ganduje.

Amma bayan watanni uku, maginin sai ya gano an baiwa wasu mutanen daban filayen da ya biya kudi, hakan yasa ya nemi a mayar masa da kudadensa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel