Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Ba Ni Rashawar N5bn," Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Femi Durotoye ya ce wani babban jami'in gwamnatin Bola Tinubu ya matsa masa kan cin hanci
- Mista Durotoye ya ce jami'in ya nemi ya kara yawan kuɗin kwangilar horas da matasa a kan shugabanci daga N1.3bn zuwa N5bn
- Ɗan siyasar ya kuma bayyana yadda aka ƙarke a kan batun bayan ya ƙi amincewa a sanya shi cutar da gwamnatin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma kwararre a fannin shugabanci, Fela Durotoye, ya fadi yadda ya kauce wa cin hanci a gwamnatin tarayya.
Ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron shekara biyu na Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito tsohon dan takarar ya ce wasu jami'an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sun yi kokarin shigar da shi badakalar kwangilar N5bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka so shirya badakala a gwamnati
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Durotoye ya ce wani babban jami’in gwamnati, wanda ya gabatar da kansa a matsayin fasto ya tuntube shi da tayin gudanar da wani shirin horar da shugabanni a fadin Najeriya.
Shirin dai zai horas da mutanen da za a zaba a dukkanin kananan hukumomi 774 cikin makonni takwas, kuma an tabbatar masa cewa an riga an ba shi kwangilar.
Bayan nazari da tantance bukatun aikin, Durotoye da tawagarsa sun gano cewa kudin da ya dace a kashe don gudanar da aikin ba zai wuce N1.3bn ba.
"An nemi na kara kudin kwangila," Durotoye
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya shaida cewa kwanaki kadan bayan ya mika adadin kudin da kwangilar da aka ba shi zai dauka, sai aka nemi ya kara.
Fela Durotoye ya ce:
"Na samu kiran taya ni murna cewa an ba ni aikin, amma suka ce kudin da nake nema ya yi kadan. Sun ce za su kara mani Naira miliyan 700 don ya zama Naira biliyan 2. Daga nan suka bukaci in fitar da takardar biyan kudi (invoice) na Naira biliyan 5."
Ya ce da ya tambayi dalilin karin kudin, musamman duba da cewa shirin yana da alaka da shugabanci na gari, sai aka tabbatar masa da cewa ba wani abu ba ne.
EFCC ta cafke wasu jami’an gwamnatin tarayya
Bayan watanni uku, aka samu labarin cewa wasu jami’an fadar shugaban kasa sun shiga hannun EFCC bisa zargin karkatar da N426m da aka ware don shirin horar da shugabanni kan dabi’u na gari.
A cewar Durotoye, wannan ya tabbatar masa da cewa kin amincewarsa da tayin cin hanci shi ne matakin da ya dace, domin da ya shiga cikin wanda EFCC za ta damke.
Ya ce:
"Abin da zai taimake ka wajen kin aikata rashawa shi ne dabi’unku na gaskiya,"
An gano tsofaffin jami'an gwamnati da rashawa
A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gano wasu daga cikin shugabannin hukumar tattara kudin haraji na jihar da karkatar da kudin jama'a.
Shugaban hukumar KIRS, Dr. Zaid Abubakar da ya bayyana haka, ya ce an samar da hanyar dakile wawashe harajin Kanawa da dabarun kara yawan kudin shiga.
Asali: Legit.ng