Gwamnatin Abba Ta Gano Inda aka Boye Biliyoyin Naira na Kudin Harajin Kano

Gwamnatin Abba Ta Gano Inda aka Boye Biliyoyin Naira na Kudin Harajin Kano

  • Hukumar KIRS ta gano asusun sirri da wasu tsirarun mutane ke amfani da su wajen karkatar da kudaden shiga na jihar Kano
  • Shugaban hukumar, Dr. Zaid Abubakar ya ce ba za a zuba idanu a rika cutar da tattalin arzikin Kano ba ta hanyar handame haraji
  • Ya ce an bullo da sabon tsarin asusun bai daya don hana satar kudaden haraji tare da sa ran samar da sama da N100bn a shekarar 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar tattara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta bankado asusun banki wasu tsofaffin jami'ai da ake amfani da su don karkatar da kudaden shiga.

Hukumar ta koka kan asarar biliyoyin Naira da su ka yi layar zana ta wadannan asusu da aka bude ba bisa ka’ida ba kafin zuwan sabon shugabancin KIRS.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Gwamna
Gwamnatin Kano ta gano wanda su ka boye harajin jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

The Guardian ta ruwaito cewa Shugaban Hukumar Tattara Haraji a Kano, Dr. Zaid Abubakar, ya bayyana wannan batu ne yayin taron bitar aikin shekarar 2024 da kuma shirin karin kudin shiga 2025 a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An dauki matakin dakile zurarewar haraji

PM Nigeria ta ruwaito Dr. Zaid Abubakar ya ce gwamnatin da ta shude ta wawure kudaden shiga da kuma rage adadin kudaden haraji da ake sa wa a asusun gwamnati.

Ya zargi tsofaffin shugabannin hukumar da aikata zamba, inda ya bayyana cewa an dauki sababbin dabarun da za su toshe duk wata kafa ta asarar haraji.

Sai dai shugaban hukumar bai bayyana adadin kudaden da aka sace ba, ko sunayen wadanda ke da alhakin tattara haraji a wancan lokaci.

Kano ta gaza kafada-da-kafada da takwarorinta

Dr. Abubakar ya jaddada cewa rashin ingantaccen tsarin haraji a baya, ya hana Kano samun damar gogayya da takwarorinta a fannin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki

A cewarsa, sabon tsarin hukumar ya bullo da asusun banki na bai daya domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, tare da hana karkatar da kudaden haraji.

Ya kara da cewa hukumar na sa ran samar da fiye da N100bn na kudaden haraji a shekarar 2025, wanda zai haura N70bn da gwamnatin jiha ta nemi a tattaro mata.

Gwamnan Kano ya amince da sake fasalin haraji

Shugaban hukumar KIRS ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sake duba dokokin haraji na jihar domin bunkasa kudaden shiga kafin karshen zangon farko na shekarar 2025.

Dr. Zaid Abubakar ya kara da cewa, hukumar ta bullo da sababbin hanyoyin tuntuba da wayar da kan masu biyan haraji domin su fahimci yadda tsarin ke tafiya.

Ya kuma jinjinawa Gwamna Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, wanda ya ce hakan ya taimaka matuka wajen saukaka aikinsu.

Gwamnatin Kano na shirin fara karbar harajin noma

Kara karanta wannan

Boko Haram ta bullo da sabuwar dabarar kashe bayin Allah, an hallaka mutane a Borno

Mai ba Gwamna Shawara na Musamman kan Haraji, Ibrahim Barde, ya bukaci hukumar ta magance wasu daga cikin matsalolin da ke hana jihar samun cikakken kudaden shiga.

A jawabinsa yayin taron, ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na nazarin yiwuwar fara karbar haraji kan amfanin gona a jihar, sai dai bai fadada magana a kan hakan ba.

Gwamnatin jihar Kano ta yi babban rashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta wayi gari da rashin daya daga cikin jami'anta, Ahmadu Haruna Zago bayan ya shafe tsawon lokaci ya na jinya.

Kafin rasuwar fitaccen dan siyasan, Danzago ya rike mukamin shugaban jam'iyyar CPC kafin 'maja' da ya samar da jam'iyya mai mulki ta APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel