Katsina: Likitan da ke Kula da Lafiyar 'Yan Ta'adda Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro

Katsina: Likitan da ke Kula da Lafiyar 'Yan Ta'adda Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar cafke wani likita da ake zargi da kula da lafiyar ƴan ta'adda a jihar Katsina da ake kuka da 'yan bindiga
  • Ana zargin likitan da ba ƴan ta'adda kulawa ciki har da wani jagoransu mai suna Usman Modi Modi da hukumomi suke nema ruwa a jallo
  • Likitan mai suna Lawan Ado ya amsa zargin da ake masa na taimakon ƴan ta'adda, inda ya ce ana biyansa kuɗi kan aikin da yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun kama wani likita mai suna Lawan Ado a jihar Katsina bisa zargin kula da lafiyar ƴan ta'adda.

Daga cikin mutanen da ake zargin likitan ya kula da lafiyarsu ciki har da wani shahararren jagoransu da ake nema ruwa a jallo mai suna Usman Modi Modi.

Kara karanta wannan

Janar Tsiga: Yadda 'yan bindiga suka shammaci jama'a, suka sace tsohon shugaban NYSC

An cafke likita a Katsina
Likita mai taimakon 'yan bindiga ya shiga hannu a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron sun kama Lawan Ado ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukansa.

Likita mai taimakon ƴan ta'adda ya shiga hannu

Bayanan sun nuna cewa likitan yana kula da ƴan bindigan da suka samu raunuka a hare-hare daban-daban.

Majiyoyi sun bayyana cewa Lawan Ado ya amsa cewa ya daɗe yana kula da lafiyar ƴan bindiga a maɓoyarsu da ke sassa daban-daban na jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa ana biyansa kuɗi idan ya yi aikinsa ciki har da magance raunukan da Usman Modi Modi ya samu bayan wani faɗa da ƙungiyar sa-kai ta Yan Kyanbara

Bincike ya kuma nuna cewa Lawan Ado ya riƙa tafiya wurare daban-daban domin kula da lafiyar ƴan bindiga, lamarin da ke nuna cewa yana taimaka musu a ayyukansu na ta’addanci.

Kara karanta wannan

Shahararrun 'yan bindiga sun tuba, sun mika makamansu ga jami'an tsaro

Jami'an tsaro na farautar miyagu a Katsina

Kamun da aka yi masa babbar nasara ce a yaƙi da ƴan bindiga a jihar Katsina, domin yana daga cikin matakan da hukumomi ke ɗauka don cafke masu taimakawa ƴan ta’adda.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano sauran mutane suke haɗa baki da shi wajen taimakon ƴan bindiga.

Ƴan bindiga sun kashe ƴan kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka wasu ƴan kasuwar tumatur a jihar Katsina.

Ƴan.bindigan sun hallaka ƴan kasuwan ne bayan sun harbi motarsu lokacin da suke tsaka da tafiya a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel