Kotu Ta Zauna kan Shari'ar Farfesa Yusuf, Ta Ki Amincewa da Bukatar Beli kan Wasu Dalilai

Kotu Ta Zauna kan Shari'ar Farfesa Yusuf, Ta Ki Amincewa da Bukatar Beli kan Wasu Dalilai

  • Babbar kotun Abuja ta sake zama kan shari'ar da ake tuhumar Farfesa Usman Yusuf da badakalar kudi lokacin yana ofis
  • Kotun ta yi watsi da buƙatar belin tsohon shugaban NHIS wanda EFCC ke tuhuma da bayar da kwangila ba bisa ƙa'ida ba
  • An gurfanar da Farfesan a gaban kotu bisa zargin almundahana, lamarin da ya haifar da cece-kuce musamman a Arewa
  • Kotun da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar yayin da ake ci gaba da sa ido kan yadda shari'arsa hukumar EFCC za ta kaya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar kotun Abuja ta yi hukunci yayin da ake shari'ar tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Kotun yayin zamanta, ta yi watsi da buƙatar belin Farfesa Usman Yusuf kan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Kotu ta ki ba da belin Farfesa Usman Yusuf
Kotun Abuja ta ki amincewa da bukatar ba da belin Farfesa Usman Yusuf. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Twitter

Musabbabin kama Farfesa Yusuf da EFCC ta yi

BBC Hausa ta ce ana tuhumarsa da bayar da kwangila ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da yake kan ragamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan cafke shi da Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa watau EFCC ta yi a karshen watan Janairun 2025.

Jami'an EFCC sun cafke tsohon shugaban NHIS ne yayin da suka kai samame gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Kamun Farfesa Yusuf ya tayar da kura musamman a Arewacin Najeriya da aka fara fargabar ana neman rufe bakin masu sukar gwamnatin Bola Tinubu ne.

Yaushe kotun za ta cigaba da sauraran shari'ar?

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ce ta gurfanar da Farfesan a gaban kotu, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a faɗin ƙasa.

Wasu na ganin kama shi ya shafi batun bi-ta-da-ƙullin siyasa da ake zargin gwamnatin Bola Tinubu da yi.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An maka Shugaba Tinubu a kotu kan badakalar kwangilar Naira biliyan 167

Rahotanni sun tabbatar da cewa Kotun ta ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 27 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Ana sa ran za a ci gaba da shari'ar a wannan rana domin sanin matakin da kotun za ta dauka.

Dattawan Katsina sun koka da kama Farfesa Yusuf

Kun ji cewa Dattawan jihar Katsina sun bukaci a saki tsohon shugaban hukumar inshora ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf ba tare da sharadi ba.

Kungiyar dattawan ta ce Farfesa Usman Yusuf bai aikata wani laifi ba face faɗin gaskiya game da halin da Najeriya ke ciki a yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.