"Mun Gano Masu Shirya wa Shugaban Hukumar Hajji Makarkashiya," Kwankwaso

"Mun Gano Masu Shirya wa Shugaban Hukumar Hajji Makarkashiya," Kwankwaso

  • Kusa a APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa shirin hana shugaban NAHCON, Abdullahi Saleh Pakistan aikinsa ba zai yi tasiri ba
  • Kwankwaso ya musanta rahoton cewa wasu masu son tafiya hajjin bana na iya rasa damar tafiya, yana mai cewa wannan tsagwaron ƙarya ce
  • Jagoran a APC ya yi zargin wasu na son kawo cikas ga shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da barazana ga gwamnatin Bola Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon kwamishinan Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi gargaɗi cewa shirin bata sunan shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ba zai yi tasiri ba.

Alhaji Kwankwaso ya yi wannan martani ne a yayin da ake rade-radin cewa wasu daga cikin masu son yin aikin hajjin 2025 na iya rasa damar tafiya sauke farali.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Kwankwaso
Kwankwaso ya soki masu sukar NAHCON Hoto: Hoto: Musa DanZaria/Hajj Chronicles
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jagora a jam'iyyar APC, ya ce rahoton karya da aka yada ya na nufin kawo cikas ga shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musa Iliyasu Kwankwaso ya kara da cewa wannan barazana ce babba ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Musa Kwankwaso ya yi martani kan sukar shugaban NAHCON

Aminiya ta wallafa cewa Kwankwaso ya bayyana cewa ƙoƙarin nuna gazawar Farfesa Pakistan na da alaka da ‘yan adawa.

Ya ce su na tsoron cewa idan aka bar shugaban NAHCON, zai kawo sauyi mai kyau, kamar yadda aka ga nasarorin da ya samu a baya.

Kwankwaso ya ce:

"Mun lura da wasu rahotanni na kafofin yada labarai da ke ikirarin cewa dubban masu son tafiya hajji na iya rasa damar yin haka. Wannan ƙarya ce kai tsaye da aka yi don kawo cikas ga shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan."

Ya kuma ce wasu ‘yan adawa na daukar nauyin marubuta don yada labaran ƙarya game da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan domin bata masa suna.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna El Rufa'i ya yi maganar shirin gwamnatin Tinubu na 'cafke' shi

Hon. Kwankwaso ya ƙaryata rahoton a kan NAHCON

Kwankwaso ya ƙara da cewa ya kamata al’umma, musamman masu son tafiya aikin hajj, su yi watsi da wannan rahoton karya da ake yada wa a kan Farfesa Abdullahi Pakistan.

Ya bayyana cewa sabon shugaban yana da kwarewar da ake bukata don gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Ya ce:

"Wannan wata dabara ce kawai ta dagula al'amura don tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ta gaza. Amma ba za su yi nasara ba. Wannan ƙarya ba za a bari ta ci gaba ba."

Kwankwaso ya ce Shugaban NAHCON ya yi martani game da zargin da aka yi masa na cewa ya soke kwangilolin kamfanonin aikin hajji biyu.

Ya bayyana cewa ainihin hukuncin soke kwangilolin ya fito ne daga hukumomin Saudiyya, wanda ke nufin ba shi da hannu a ciki.

Ana zargin Rabiu Kwankwaso zai fice daga APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

"Dalilina na sukar BolaTinubu a baya," Hadimin shugaban kasa

Ya ce Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC domin cimma burinsa na siyasa, inda ya bayyana cewa Kwankwaso zai samu damar taimakawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zarce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel