'Yan Majalisar Wakilai Sun Fara Tattake Wuri kan Kudirin Harajin Tinubu, Bayanai Sun Fito

'Yan Majalisar Wakilai Sun Fara Tattake Wuri kan Kudirin Harajin Tinubu, Bayanai Sun Fito

  • Majalisar Wakilai ta fara muhawara kan kudirin sauya fasalin harajin da ake ta ka-ce-na-ce a kansa a zamanta na yau Laraba, 12 ga watan Fabrairu
  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika kudirin dokokin guda huɗu ga Sanatoci da 'Yan Majalisar Tarayya tun a shekarar 2024
  • Tun bayan miƙa kudurin, ƴan Najeriya suka fara sukarsa musamman yan Arewa waɗanda ke ganin a shirya sababbin dokokin ne domin yi masu illa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta fara muhawara a ranar Laraba kan sababbin dokokin haraji guda huɗu da Bola Tinubu ya aike mata a bara.

Idan ba ku manta ba shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sababbin dokokin harajin ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa a shekarar 2024.

Majalisar Wakilai.
Majalisa ta fara muhawara kan dokoki 4 na gyara fasalin haraji a Najeriya Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Yadda Bola Tinubu ya miƙa kudirin haraji

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Channels tv ta tattaro cewa waɗannan dokoki sun tsallaka zuwa karatu na biyu a zauren majalisar wata shida bayan da shugaba Tinubu ya gabatar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko dai Tinubu ya fara yunƙurin gyara fasalin haraji ne bisa shawarwarin kwamitin gyaran dokokin haraji da manufofin kuɗi karkashin jagorancin Taiwo Oyedele.

Sababbin dokokin harajin Tinubu

Dokokin guda huɗu da ƴan Majalisa suka fara tattake wuri a kansi yau Laraba, 12 ga watan Fabrairu, 2025 sun haɗa da:

1. Dokar haraji ta Najeriya 2024

2. Dokar gudanar da haraji

3. Dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta Najeriya

4. Dokar kafa hukumar hadin gwiwa wajen karɓar haraji

Sai dai, wadannan sababbin dokokin da a dunƙule aka rika kiransu da kudirin sauya fasalin haraji sun haifar da ce-ce-ku-ce mai yawa a ƙasar nan.

Sun fuskanci suka da ƙalubale daga bangarori daban-daban kamar gwamnonin Arewa da ‘yan adawa waɗanda suka nuna rashin amincewarsu da lamarin.

Kara karanta wannan

Mummunar rigima ta kaure tsakanin ƙungiyoyi 2 kan 'kuɗi', an kashe mutane sama da 10

Majalisa ta fara tattake wuri kan kudirin

Galibin masu sukar kudirin harajin sun bukaci a janye shi daga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan a sake zama don warware wuraren da ke da matsala.

A halin yanzu, Majalisar Wakilai ta fara tafka muhawa kan dokokin guda huɗu a zaman yau Laraba a Abuja, rahoton Daily Trust.

'Yan majalisa sun amince da bukatar Tinubu

Ku na da labarin Majalisar wakilai ta amince da buƙatar mai girma shugaban ƙasa na ƙara kasafin kudin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.

Wannan mataki ya samo asali ne daga ƙarin kuɗin shiga da hukumomin gwamnati suka samar, ciki har da Naira tiriliyan 1.4 daga Hukumar FIRS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel