Gwamna zai Karya Farashin Abinci Warwas saboda Azumin Watan Ramadan
- Gwamnatin Jihar Neja za ta dauki matakin rage farashin kayan abinci domin saukaka wa jama’a a watan Ramadan da ake shirin shiga
- Gwamna Umaru Bago ya ce jihar ta girbi fiye da ton miliyan 1 na masara, kuma ana amfani da kamfanin Niger Foods wajen daidaita farashi
- Gidauniyar Bill Gates ta yabawa gwamnatin Umaru Bago bisa kokarinta na bunkasa noma da rage talauci a tsakanin al'ummar jihar Neja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja - Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana shirin samar da tallafi domin rage farashin kayan abinci yayin azumin watan Ramadan mai zuwa.
Matakin na da nufin tabbatar da cewa al’ummar jihar, musamman masu karamin karfi, sun samu sauki wajen sayen kayan abinci a lokacin azumi.

Asali: Twitter
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Balogi Ibrahim ya wallafa jawabin da gwamnan ya yi a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan jihar, Umaru Bago, ya bayyana haka ne lokacin da wata tawaga daga Gidauniyar Bill Gates ta kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar da ke Minna.
Matakin rage farashin abinci a azumi
Gwamna Umaru Bago ya ce daya daga cikin manyan matakan da gwamnatinsa ke dauka domin tallafawa al’ummar jihar shi ne rage tsadar kayan abinci.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta fitar da wasu tsare-tsare da za su sa kayan abinci su yi sauki domin saukaka wa jama’a a watan azumin Ramadan.
A cewarsa, jihar Neja ta samu babbar nasara a harkar noma, inda aka girbi fiye da ton miliyan 1 na masara.
Ya kara da cewa haka ne ya sa ake amfani da kamfanin Niger Foods domin tabbatar da daidaiton farashi a kasuwanni, ba kawai a Neja ba har ma a wasu sassan Najeriya.

Kara karanta wannan
"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki
Bukatar hadin gwiwa kan noma
Gwamnan ya bukaci Gidauniyar Bill Gates da ta kara karfafa dangantaka da gwamnatin jihar wajen habbaka noman amfanin gona da kiwon dabbobi.
Ya ce jihar Neja tana shirin daga yawan lokacin noman da ake yi a shekara daga sau daya zuwa sau uku, domin kara yawan amfanin gona da inganta tattalin arziki.
Ya kuma jaddada muhimmancin amfani da noman rani ta hanyar amfani da hanyoyin ban ruwa, wanda hakan zai taimaka wajen dakile illar sauyin yanayi da rage dogaro da damina kadai.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na bukatar hadin gwiwa da gidauniyar Gates a fannoni daban-daban, ciki har da samar da gidaje da kuma bunkasa kiwon kifi a jihar.
Gidauniyar Gates ta yabi gwamna Bago
Jagoran sashen raya harkokin noma na Gidauniyar Gates, Obai Khalifa, ya ce tun bayan kafa gidauniyar shekaru 25 a baya, suna kokarin inganta rayuwar jama’a ta hanyar bunkasa noma.
Ya bayyana cewa noma ba wai don samar da abinci kadai take da mahimmanci ba, akwai rawar da take takawa wajen samar da wadataccen abinci mai gina jiki da samar da tsaro.
Shi ma babban jami’in shirye-shiryen noma na Gidauniyar Gates a Afrika, Audu Grema, ya jinjinawa Gwamna Umaru Bago bisa kokarinsa na bunkasa fannin noma.
Audu Grema ya ce hakan zai taimaka wajen rage talauci da samar da wadataccen abinci ga jama’a.
Za a bukasa noman dabino a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta yi hadaka da kasar Saudiyya domin habaka noman dabino.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi masana noman dabino daga kasar Saudiyya a birnin Dutse.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng