Faɗa Ya Ɓarke a Jami'ar Najeriya, Ɗaliba Ta Yi wa Malami Kaca Kaca a Bidiyo

Faɗa Ya Ɓarke a Jami'ar Najeriya, Ɗaliba Ta Yi wa Malami Kaca Kaca a Bidiyo

  • An samu hatsaniya sashen adabi na Jami’ar UNIZIK, Awka, bayan wata daliba ta kai wa malami hari tare da gartsa masa cijo
  • An ce rikicin ya kaure ne lokacin da malamin ya katse dalibar a lokacin da take daukar bidiyon rawa na TikTok a harabar jami’ar
  • Jami’an tsaro sun tabbatar da lamarin yayin da aka samu hotuna da bidiyo da suka nuna fadan da raunin da malamin ya samu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Rikici ya barke a sashen adabi na jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), da ke Awka, bayan wata daliba ta kai wa malami hari, har ta cije shi.

Lamarin ya faru ne a harabar jami’ar yayin da malamin, Dr. Chukwudi Michael, ya katse dalibar a lokacin da take daukar bidiyon rawa na TikTok.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

Daliba ta gartsawa malami cizo yayin da rigima ta kaure tsakaninsu kan TikTok
Fada ya kaure tsakanin malami da wata dalibar jami'ar UNIZIK kan TikTok. Hoto: @Daffydrejr
Asali: Twitter

Daliba ta ci kwalar malaminta a jami'ar UNIZIK

Shaidun gani da ido sun ce dalibar tana rawa yayin da wani ke daukarta a bidiyo lokacin da Michael ya yi yunkurin wucewa ta gabanta, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Malamin ya taba ta a kafaɗa yana ce mata ‘yi hakuri, zan wuce,’ amma sai ta fusata tana cewa, ‘ka duba yadda ya bige ni!’” inji wani ganau.

Rigimar ta rikide zuwa fada yayin da dalibar ta ci kwalar malamin jami'ar cikin fushi, kuma ta ki saki, duk da kokarin da wasu suka yi na shiga tsakani.

Jami'an tsaron jami'ar sun tabbatar da rikicin

Bidiyon rikicin ya bazu a shafukan sada zumunta, inda aka ga dalibar tana ta cece-kuce da malamin, tana ikirarin cewa ya buge ta da gangan.

A wani bidiyo na daban, an ga malamin yana daga hannayensa a matsayin kariya yayin da dalibar ta ci gaba da rike shi da karfi.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun firgita da cewa 'Allah ya yi wahayi' makiyaya za su kai hari

Jami’in tsaro na jami’ar, Ken Chukwurah, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa bincike na gudana domin gano hakikanin abin da ya faru.

UNIZIK: An gano dalibar 'yar aji uku ce

Ya bayyana cewa malamin ya ji dalibar tana zagin sa bayan ya wuce, sannan ya dawo domin tabbatar da ko tana cikin ajinsa.

A cewar rahotanni, malamin ya yi yunkurin karbar wayarta don hana ta yada a bidiyon da ta dauka a TikTok, amma ta farmake shi, har da cijo.

Hotunan da suka karade yanar gizo sun nuna alamun cizo a hannun malamin.

Rahotanni sun kuma ce dalibar tana aji uku ce a tsangayar tarihi da nazarin al’amuran duniya, kuma diyar wani malami a sashen injiniyanci na jami’ar ce.

Kalli bidiyon rigimar, da wata @Hybrid_Ola ta wallafa a shafinta na X.

'Ya kamata jami'ar ta hukunta dalibar' - SYM

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

A zantawarmu da Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban hakimin Mani da ke jihar Katsina, ya ce dalibar ta nuna tsaurin ido sosai, yadda ta ci kwala da cizon malamin.

Wakilin daliban ya ce:

"Mu kaddara ma malamin ne ke da laifi, wannan ya isa ta ci zarafinsa a gaban dalibai har ma a rika ba ta baki don ta sake shi ta ki saurarar kowa?
"Ai malami ya wuce wasa. Shi ya sa da yawan dalibai kan gama makaranta ba tare da amfana da abin da malaman suka koyar ba, saboda sun raina su, ba su dauke su a bakin komai ba.
"Ta ya don Allah dalibi zai girmama ilimi ace yana cin kwalar malami, yana cizonsa, yana zargi da fada masa bakaken maganganu, kuma duk a kan TikTok?"

Sanusi Ya'u ya ce dandalin TikTok yanzu ya koma tamkar annoba, inda ya nemi gwamnati ta sanyawa dandalin doka don tabbatar da tarbiyar matasan kasar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun raunata 'yan sanda yayin da suka daku da juna, an ladabtar da jami'ai

"Akwai bukatar jami'ar UNIZIK ta gaggauta daukar mataki a kan dalibar nan. Lallai ne a hukuntata, don ya zama darasi ga kowa. Sannan idan aka samu malamin da laifi, shi ma a hukunta shi. Amma abin da dalibar ta yi ya yi muni."

- Sanusi Ya'u.

Daliba ta jagoranci yunkurin fille kan malaminta

A wnai labarin, mun ruwaito cewa, wata daliba da sauratinta a kwalejin polytechnic da ke Kano sun yi yunkurin fille kan wani malamin makarantar.

Hukumar makarantar ta sanar da cewa saurayin da dalibar sun je har ofishin malamin da nufin kashe shi, amma Allah bai ba su sa'a ba, kuma an gagara kama su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.