Dangote Ya Hakura da Naira biliyan 10, Ya Sauke Farashin Dizil a Najeriya

Dangote Ya Hakura da Naira biliyan 10, Ya Sauke Farashin Dizil a Najeriya

  • Matatar man Dangote ta rage farashin litar dizil daga N1,075 zuwa N1,020 domin saukakawa masana’antu da 'yan Najeriya
  • Dangote ya ce tun bayan da ya fara samar da dizil, farashin ya sauka sau uku daga N1,700 zuwa N1,020, kuma zai ci gaba da sauka
  • Masanin tattalin arziki, Ken Ife, ya ce Dangote ya sadaukar da fiye da Naira biliyan 10 domin tabbatar da daidaituwar farashin mai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar dizil daga N1,075 zuwa N1,020 domin tallafa wa abokan hulda da ‘yan Najeriya baki daya.

Matatar ta bayyana cewa tun bayan da ta fara samar da dizil a watan Janairun 2024, farashin ya sauka sau uku daga N1,700 zuwa N1,020.

Dangote ya yi magana da ya sauke farashin litar dizal a Najeriya
Dangote ya sanar da sauke farashin litar dizal daga N1,075 zuwa N1,020. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Matatar Dangote ta rage farashin dizil

Kara karanta wannan

Faɗa ya ɓarke a jami'ar Najeriya, ɗaliba ta yi wa malami kaca kaca a bidiyo

Matatar Dangote ta ce wannan rage farashin zai kawo wa masana’antu da masu amfani da dizal sauki a harkokinsu na yau da kullum, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rage farashin N55 da aka yi na baya-bayan nan na dizil ya biyo bayan bayanin Ken Ife, masanin tattalin arziki, kan irin gudunmuwar da kamfanin ya bayar.

Ken Ife ya ce Dangote ya hakura da fiye da Naira biliyan 10 domin tabbatar da cewa farashin mai ya kasance iri ɗaya a duk fadin ƙasar.

Dangote zai ci gaba da rage farashi

A lokacin bikin Kirsimeti, lokacin da ake yawan fama da karancin mai, Dangote ya rufe gibin farashin da kansa don gujewa tsadar kayan abinci.

Kan Ife ya yabawa kamfanin Dangote bisa kafa sabon mizani a bangaren makamashi, tare da bunkasa damar samun kudaden shiga ta hanyar fitar da mai.

Kara karanta wannan

CBN ya kawo sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi wajen aiki da ATM

Kamfanin ya ce zai ci gaba da saukaka farashin domin tallafawa tattalin arziki da rage nauyin da ke kan masu amfani da dizal.

Dangote ya kara sauke farashin fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta saukar da farashin mai daga N950 zuwa N890, saboda faduwar farashin danyen mai.

Kamfanin ya yi kira ga masu gidajen mai da su tabbatar da cewa ragin ya kai ga talakawa domin rage musu wahalhalu da nauyin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.