'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Yobe, Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Yobe, Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda

  • Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta yi rashin biyu daga cikin jami'anta bayan wasu ƴan bindiga sun hallaka su har lahira
  • Ƴan bindigan waɗanda ake zargin ƴan fashi da makami ne sun hallaka ƴan sandan ne a ƙaramar hukumar Fune ta jihar Yobe
  • Ɗaya daga cikin ƴan sandan da aka.kashe, ya rasa ransa lokacin da yake bakin aikinsa bayan ya je cafke wani da ake zargi da aikata laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Wasu miyagun ƴan bindiga da ake zargin ƴan fashi da makami ne sun hallaka jami'an ƴan sanda biyu a jihar Yobe.

Ƴan bindigan sun hallaka ƴan sandan ne waɗanda ke aiki a ofishin ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Fune a jihar Yobe.

'Yan bindiga sun hallaka sun 'yan sanda a Yobe
'Yan bindiga sun hallaka jami'an 'yan sanda a Yobe Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce harin farko ya faru ne a ƙarshen watan Janairu 2025, inda wata ƙungiyar ƴan fashi ta kashe DSP Ali Pindar, wanda ke aiki a ofishin ƴan sanda na Kolere.

Kara karanta wannan

Shahararrun 'yan bindiga sun tuba, sun mika makamansu ga jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka hallaka ƴan sanda

Majiyoyi sun bayyana cewa DSP Ali Pindar ya kama wani shugaba a cikin ƴan fashi a yankin, sannan ya miƙa shi zuwa ofishin ƴan sanda na Damagum da ke ƙaramar hukumar Fune.

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu, inda daga baya aka bayar da belinsa.

"Bayan dawowarsa, mutumin da ake zargin ya tattara wasu ƴan fashi suka kai hari kan DSP Ali Pindar, inda suka kashe shi, yayin da wani sufeta ya ji rauni a harin."

- Wata majiya

Wata majiya ta ce lamarin na biyu ya auku ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu, bayan DSP Jantuku Philibus, wanda ke kula da ofishin ƴan sanda na Kolere, ya je kama wani mutum da ake zargi da aikata laifi.

Sai dai, wanda ake zargin tare da taimakon abokansa ƴan fashi, sun farmaki jami’in ƴan sandan tare da kashe shi har lahira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi barna a Gombe, sun hallaka malamin addini

Majiyoyi sun bayyana cewa, kafin DSP Jantuku Philibus ya mutu, ya samu nasarar kashe ɗaya daga cikin ƴan fashin.

Duk da haka, sauran ƴan fashin sun yi masa taron dangi, inda suka hallaka shi bayan ya samu raunuka iri-iri.

Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce jami’an biyu sun gamu da ajalinsu ne a ƙoƙarin kama waɗanda ake zargi, bayan sun yi musu taron dangi.

A baya-bayan nan, yankin Fune ya fuskanci hare-haren ƴan fashi da makami, da kuma sace mutane don neman kuɗin fansa.

Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jiha Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ƙaramar hukumar Rabbah, sun hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng