Gwamna Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Abin da Sojoji Suke Bukata don Magance Rashin Tsaro
- Gwamnan jihar Kwara ya taɓo batun maganar rashin tsaro wacce ta ƙi ci ta ci cinyewa a ƙasar nan har na tsawon shekaru
- Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana cewa idan ana son magance matsalar, dole ne ka da a maida hankali kan siyo makamai kaɗai
- Gwamnan ya bayyana cewa ana buƙatar samar da kayayyakin more rayuw a domin sojoji su ji daɗin aikin yaƙi da miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi magana kan ƙoƙarin da sojoji ke yi domin magance rashin tsaro da ake fama da shi.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya tana buƙatar fiye da makamai domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan.

Asali: Facebook
Wace shawara gwamnan Kwara ya ba da?
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da ginin hedkwatar rundunar 22 Armoured Brigade wacce aka yi wa gyara da ke Sobi, Ilorin, babban birnin jihar Kwara, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa siyo makamai ba shi ne kawai mafita ba a ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro.
"Ba wai kawai siyo makamai ba ne mafita, dole ne a samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa domin sojoji su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."
- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
Gwamna Abdulrahman ya yabawa sojoji
Gwamna Abdulrahman ya ƙara cewa gyaran wanda sojojin Najeriya suka aiwatar, ya yi daidai da manufar babban hafsan sojojin ƙasa, wacce ke ƙarfafa al’adar kula da kayan aiki.
Bayan haka, Gwamna Abdulrahman ya ƙaddamar da sababbin motocin aiki guda uku da babura guda 10, wadanda gwamnatin jihar ta bayar domin inganta ayyukan rundunar.
A nasa ɓangaren, babban kwamandan runduna ta biyu ta sojojin Najeriya da ke Ibadan, Manjo Janar Obinna Onubogu, ya godewa gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar.
Ya ce goyon bayan da gwamnan ke bayarwa yana ƙarfafa ƙarfin rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Shi ma kwamandan 22 Armoured Brigade, Manjo Janar Oluwafemi Williams, ya bayyana cewa ya sake fasalin hedikwatar rundunar ne domin ta samu ingantaccen yanayin aiki ga jami'ai da sojojin da ke cikinta.
Majalisa ta buƙaci a tura sojoji Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta tura ƙarin jami'an tsaro zuwa yankunan da ke fama da rashin tsaro a Borno.
Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin da ta ba da kayan agaji ga mutanen da matsalar hare-haren ƴan ta'adda ta shafa a yankunan na jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng