Mahaifiya Ta Sayar da Jaririnta Mai Kwanaki 11 da Haihuwa

Mahaifiya Ta Sayar da Jaririnta Mai Kwanaki 11 da Haihuwa

  • Rahotanni sun nuna ’yan sanda sun cafke wata mahaifiya da wasu mata da ke da hannu a sayar da jariri ɗan kwanaki 11 a Jihar Delta
  • Mahaifiyar jaririn ta ce an yaudareta ta sayar da ɗanta kan N600,000 yayin da wasu suka sayar da shi a kan Naira miliyan hudu
  • Bayan samun nasarar kama matan, rundunar ’yan sanda ta ce za ta tashi tsaye domin dakile aika-aikar fataucin jarirai a Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ta cafke wasu mata uku da ake zargi da sayar da jariri mai kwanaki 11 kan kuɗi har Naira miliyan hudu.

Kakakin rundunar, Edafe Bright, ya bayyana cewa an kama matan ne bayan bincike ya nuna cewa suna da hannu a mummunan fataucin jarirai.

Kara karanta wannan

CBN ya kawo sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi wajen aiki da ATM

Yan sanda
An kama mahaifiya da ta sayar da danta a Delta. Hoto: @Brightgoldenboy
Asali: Twitter

A wani bidiyo da kakakin ya wallafa a X, ya ce mahaifiyar jaririn mai suna Rachael ita ce ta fara sayar da ɗanta bayan wata mata ta lallashe ta da cewa za ta taimaka mata bayan haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sayar da jariri a jihar Delta

Bayan kammala binciken farko, mahaifiyar jaririn, Rachael, ta bayyana cewa ta sayar da jaririn ne kan N600,000 amma daga baya aka sake sayar da shi kan Naira miliyan 4.

Ta ce wata mata ce ta zo gare ta tana nuna damuwa game da halin da take ciki bayan ta haihu, sannan ta shawo kanta ta sayar da jaririn ga wata mace da ke harkar fataucin jarirai.

Bayan haka ne makwabta suka fara zargin rashin ganin jaririn bayan haihuwarsa, lamarin da ya sa suka sanar da ’yan sanda.

An kama masu hannu a fataucin jaririn

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Binciken ’yan sanda ya nuna cewa Rachael ta karɓi N600,000 kacal a kuɗin da aka sayar da jaririn, yayin da wanda ta sayar wa jaririn ta sake sayar da shi ga masu fatauci a kan N3.5m.

A cewar kakakin rundunar ’yan sandan:

"Mun fahimci cewa fataucin jarirai yana ƙaruwa, kuma za mu dauki matakan dakile mummunan aiki."

Ya ƙara da cewa kwanan nan rundunar ta kama wasu mata uku da ke kokarin tafiya da wasu jarirai uku zuwa Abuja ta filin jirgin saman Asaba.

'Yan sanda za su dakile fataucin jarirai

Edafe Bright ya ce rundunar za ta tashi tsaye domin tabbatar da cewa irin wannan cin zarafin jarirai ya tsaya cak.

The Nation ta wallafa cewa kakakin 'yan sandan ya ce:

“Mahaifiyar jaririn ta sayar da shi ga wata mata, ita kuma ta sake sayar da shi kan miliyan 4, duk da cewa ta ce Naira miliyan 3.5 ne kawai ta karɓa.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

"Abin bakin ciki shi ne, mahaifiyar jaririn ba ta ma samu fiye da N600,000 ba daga cikin wannan kuɗi.”

A halin yanzu dai an ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, tare da fatan dawo da jaririn ga iyayensa na asali da kuma gurfanar da duk masu hannu a aika-aikar a gaban kotu.

Ana ba tubabbun 'yan Boko Haram horo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta yi bayani a kan shirin da ta ke na musamman kan ba tubabbun 'yan Boko Haram horo na musamman.

Rundunar tsaron ta ce a yanzu haka ta ware 'yan kungiyar Boko Haram 800 da suka tuba domin ba su horo kafin a dawo da su cikin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng