Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

Rundunar 'yan sanda a Kano ta yi holen wani Farfesa Solomon Musa Tarfa da aka kama a watan Disamban 2019 da ake zargi da kafa gida marayu, ‘Du Mercy Children Development Ministry’ ba tare da samun izini daga gwamnati ba.

'Yan sanda da wasu jami'an tsaro sun kai sumame a gidan marayun ne a ranar 25 ga watan Disamban 2019 inda suka ceto yara 19 da suka hada da mata da maza masu shekaru daban-daban. Hakan na zuwa ne bayan gidan marayun ya kwashe kimanin shekaru 20 yana aiki.

Da ya ke zantawa da manema labarai a jiya, Kakakin 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi ikirarin cewa Farfesa Tarfa ya hada baki da wani likita, Chidi Christopher da ke da asibiti a Nomansland a Kano inda suke sace jarirai bayan an haife su a asibitinsa.

Ya yi ikirarin cewa Dr Nwoye da yanzu ake nema ya taimaka wurin nemo mata masu ciki da ya bawa kulawa har suka haihu bayan haka kuma sai ya karbi jariran ya mika wa gidan marayun.

'Yan sandan sun kuma zargi matar Farfesa Tarfa, Mercy ta taimakawa wurin nema yara ta wasu hanyoyin da suka saba wa doka.

DUBA WANNAN: Hotunan ziyarar da Ahmed Musa da 'yan kungiyarsa suka kai wa yariman Saudiyya

Kakakin 'yan sandan ya ce, "A kokarin da muke na gano yaran da suka bace, a ranar 25 ga watan Disamban 2019, mun samu ingantaccen bayani cewa wani Farfesa Solomon Musa Tarfa da ke zaune a No. 15 Iroko Avenue, Nomansland a Kano yana da gidan marayu mai suna Du Mercy Children Development Ministry ba tare da izinin hukuma ba.

"Yana amfani da gidan marayun don ajiye yara maza da mata da ake kyautata zaton ya samo su ne ba bisa ka'ida ba."

Da ya ke mayar da ba'asi kan zargin, Farfesa Tarfa ya ce an yi wa gidan marayun shi rajista da hukumar CAC, inda ya ce wasu da ke neman bata masa suna ne suka yi masa cinne.

Sai dai ya ki bayyana hanyoyin da ya ke amfani da shi wurin samo yaran inda ya ce lauyansa ne kadai zai iya amsa tambayoyi kan yadda ya ke samo yaran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel