An Kama Mai Safarar Makamai Yana Shirin Mika Bindigogi ga 'Yan Ta'adda

An Kama Mai Safarar Makamai Yana Shirin Mika Bindigogi ga 'Yan Ta'adda

  • Sojojin Najeriya karkashin Operation Fansan Yanma sun garkame wani mutum da ake zargi da safarar makamai a Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne yana kokarin kai wa ‘yan ta’adda makamai bayan an zafafa kai musu hari
  • Biyo bayan nasarar, 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun jinjinawa kokarin sojojin wajen dakile safarar makamai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Sojoji da ke aiki karkashin Operation Fansan Yanma sun kama wani da ake zargi da safarar makamai yayin da yake kokarin tserewa da makamai da za a kai wa ‘yan ta’adda.

Lamarin ya faru ne a daren da sojoji suka kai hari kan 'yan ta'adda a Nasarawa Burkullu da ke jihar Zamfara, bayan samun sahihan bayanan sirri kan safarar makaman.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Makamai
An kama mai safarar makamai a Zamfara. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya wallafa yadda aka kama mutumin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa wanda aka kaman sanannen mai safarar makamai ne daga karamar hukumar Anka, wanda ke samar da makamai ga ‘yan bindiga.

Sojoji sun dakile safarar makamai

Bayan samun bayani kan yunkurin mai safarar makaman, sojoji sun yi wa hanyar da yake bi kwanton bauna a Nasarawa Burkullu.

Da ya fahimci cewa sojoji sun yi masa kwanton bauna, sai ya yi kokarin tserewa amma sojojin suka yi sauri suka cafke shi shi.

Bincike ya tabbatar da cewa mutumin yana dauke da mugayen makamai da harsasai da aka shirya kai wa ‘yan bindiga da ke cikin mawuyacin hali sakamakon matsin lambar da sojoji ke yi musu.

Nasarar da ake samu kan 'yan ta'adda

Tun bayan da sojojin Najeriya suka fara kai hare-hare a dazukan Zamfara da sauran yankuna, rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’adda na fama da matsalar karancin makamai.

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Wasu daga cikinsu sun fara mika wuya, yayin da wasu ke ta kokarin samo makamai daga masu safarar muggan kayan aiki irin wannan da aka kama.

Dakarun Operation Fansan Yanma sun jaddada cewa za su ci gaba da sintiri da kai hare-hare domin hana safarar makamai ga ‘yan ta’adda.

Jama’a sun jinjinawa kokarin sojoji

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa mutane sun yi farin ciki da kokarin da sojoji ke yi domin murkushe ‘yan ta’adda.

Wasu daga cikin jama’ar Zamfara sun yaba da yadda rundunar sojin ke kai farmaki a yankunan da ke fama da matsalar tsaro, inda suka bukaci a kara tashi tsaye domin kawo karshen matsalar.

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda da kuma hana samar musu da makamai, domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

Ana ba tubabbun 'yan Boko Haram horo

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji a Zamfara, sun kaddamar da hari

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya na daukar matakai kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya ga jami'an tsaro.

Kimanin mayakan Boko Haram 129,000 ne suka tuba amma an zakulo 800 domin ba su horo na musamman a kokarin canja musu tunani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng