Mayakan Boko Haram 129,000 Sun Tuba, Ana ba 800 Horo na Musamman

Mayakan Boko Haram 129,000 Sun Tuba, Ana ba 800 Horo na Musamman

  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa tsofaffin mayakan Boko Haram kimanin 800 na cikin shirin gyaran hali a Najeriya
  • Tsofaffin 'yan ta'adda kusan 129,000 daga cikin 'yan Boko Haram da iyalansu sun mika wuya ga dakarun rundunar sojin Najeriya
  • Sojojin Najeriya sun bayyana cewa ana amfani da dabaru daban daban wajen ganin an kawar da 'yan Boko Haram da sauran miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa tsofaffin mayakan Boko Haram 800 da suka mika wuya suna cikin wani shirin gyaran hali da ake yi musu tsawon shekara guda.

Ana sa ran cewa za a sauya musu tunani ta yadda 'yan ta'addar za su nisanci ta'addanci idan suka kammala shirin.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Janar Musa
An ba tubbabbun Boko Haram horo. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Babban jami’in horo da ayyukan yaki na rundunar tsaro, Manjo Janar Emeka Onumajuru ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daga cikin mutum 129,000 da suka mika wuya ga gwamnati, an tantance 800 ne kacal don shiga shirin gyaran hali bayan cikakken bincike a kansu.

Shirin gyara halin 'yan Boko Haram

Manjo Janar Onumajuru ya ce ana aiwatar da shirin gyaran halin ne a karkashin Operation Safe Corridor, wanda ke daukar tsawon shekara guda.

Ya ce ana gudanar da shirin ne ta hannun kwararru, kuma ana amfani da matakai na musamman donmin tabbatar da cewa tubabbun mayakan sun shiryu sosai kafin a sake su cikin al’umma.

Yadda ake zabo tubabbun Boko Haram

Babban jami’in tsaron ya ce daga cikin mutum 129,000 da suka mika wuya, ba duka ne ke shiga shirin gyaran hali ba.

Kara karanta wannan

Mummunar rigima ta kaure tsakanin ƙungiyoyi 2 kan 'kuɗi', an kashe mutane sama da 10

A cewarsa, ana bincike sosai domin bambance wadanda suka cancanta, inda aka tantance mutum 800 kacal a yanzu.

Ya kara da cewa wadanda ake zargi da laifuffuka masu girma ana tsare da su a wuraren da suka dace, yayin da kotu ke cigaba da tantance su domin hukunci.

Sojoji na amfani da dabaru daban-daban

A cewar Onumajuru, rundunar sojojin Najeriya na amfani da dabaru biyu domin kawo karshen ta’addanci—na yaki da na gyara.

Ya bayyana cewa ba za a iya samun nasarar yaki da ‘yan ta’adda da karfi kadai ba, dole ne a hada dabarun soji da hanyoyin sulhu kamar gyaran hali da mayar da tubabbun ‘yan ta’adda cikin al’umma.

The Cable ta wallafa cewa gwamnati na kokarin tabbatar da cewa wadanda aka gyara wa hali ba za su sake komawa ta’addanci ba.

Ya kuma jaddada cewa suna amfani da hanyoyin zamani wajen sa ido kan shirin domin tabbatar da ingancinsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

An kama dan bindiga a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama wani dan ta'adda a jihar Zamfara bayan harsashi ya kare masa.

'Dan ta'addar ya shiga hannu ne yayin da harsashi ya kare masa yana tsaka da musayar wuta da dakarun rundunar sojin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng