'Me Suke Kullawa?': Atiku Ya Ja Zugar Manyan 'Yan Siyasa, Sun Gana da Obasanjo
- Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo domin ganawar sirri a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
- An ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Obasanjo ne bisa rakiyar wasu kusoshin PDP, ciki har da Aminu Tambuwal
- Surajo Caps ya kawo dabarar kayar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa, inda ya nemi hadin kan 'yan jam'iyyun adawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jagoranci tawaga zuwa Abeokuta domin ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
An rahoto cewa Atiku ya isa ginin babban dakin karatu na Obasanjo (OOPL) tare da tawagarsa da misalin karfe 12:36 na ranar Litinin.

Source: Twitter
Atiku Abubakar ya ziyarci Obasanjo a Ogun
Tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke, da Sanata Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan Sokoto, ne suka yi wa Atiku rakiya, inji rahoton Daily Trust.
An ce Otunba Oyewole Fasawe, na hannun damar Obasanjo ne ya tarbi Atiku kafin su shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasar.
Ba a bayyana manufar taron ba, amma ana ganin wannan ganawar tana cikin shirye-shiryen ‘yan hamayya na tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
Alakar Atiku da Olusegun Obasanjo
Atiku ya yi wa Obasanjo mataimakin shugaban kasa daga Mayun 1999 zuwa Mayun 2007, lokacin mulkinsu na shekara takwas.
Channels TV ta rahoto cewa a zaben 2023, Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa a PDP, amma Shugaba Bola Tinubu na APC ya kada shi.
Atiku, mai shekaru 78, ya kwashe kimanin shekaru 30 yana neman kujerar shugaban kasa a Najeriya, sai dai har yanzu bai samu nasara ba.
An kawo dabarar kayar da Tinubu a 2027
A zantawarmu da Surajo Caps, wani dan PDP daga Bauchi, ya nemi Peter Obi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da su hade da Wazirin Adamawa gabanin 2027.
Surajo Caps ya ce yana da tabbacin cewa Atiku Abubakar zai iya lallasa shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, musamman idan ya samu goyon bayan 'yan adawa.
"Duk masu son neman takarar shugaban kasa, da masu son kalubalantar wannan gwamnatin, su kalli kasar, su kalli karfin APC, su kalli halin da talakawa suke ciki.
"Su tausayawa talakawa fiye da bukatar kansu, su hada hannu karfi da karfe, su taimaki Atiku su mara masa baya, to in sun yi haka, tarihi ba zai manta da su ba."
- Surajo Caps.
Atiku ya hadu da Sanata Aishatu Binani
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci Sanata Aishatu Dahiru Binani a Abuja.
Ziyarar Atiku ga Sanata Binani ta haifar da cece-kuce kan yiwuwar haɗin kai tsakaninsu domin shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

