Atiku zai kaiwa Obasanjo ziyara a yau

Atiku zai kaiwa Obasanjo ziyara a yau

- Atiku Abubakar zai gana da tsohon mai gidansa Obasanjo a yau

- Rahotanni sun ce 'yan kungiyar Afenifere ne suka shirya ganawar tsakanin 'yan siyasan biyu da suka dade basu shiri

- Ana kyautata zaton ganawar ba za ta rasa nasaba da babban zaben 2019 mai zuwa ba

Rahoton da muka samu daga Vanguard ya bayyana cewar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar zai ziyarci tsohon mai gidansa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a yau.

Atiku ya kaiwa Obasanjo ziyara
Atiku ya kaiwa Obasanjo ziyara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

Wannan ziyarar itace ziyara itace haduwa ta farko tsakanin tsohon shugaban kasar da tsohon mataimakinsa bayan Atiku ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar na PDP a zaben 2019.

Alakar da ke tsakanin mutanen biyu ta lalace ne tun lokacin da Atiku ya taka muhimmiyar rawa wajen hana Obasanjo zarcewa kan mulki karo na uku a lokacin da ya ke mataimakinsa.

Duk da cewar Obasanjo ya yi rantsuwar cewar ba zai taba marawa Atiku baya ba domin ya zama shugaban kasa, ba abin mamaki bane yanzu ya canja ra'ayinsa saboda baya boye rashin gamsuwarsa da irin kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar kungiyar Yarabawa ta Afenifere da suka ziyarci Obasanjo a ranar Talata ne suka bukaci ya gana da tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel