'Barazanar Tsaro' ta Hana Kashim Shettima Komawa Gidansa a Aso Villa a Abuja

'Barazanar Tsaro' ta Hana Kashim Shettima Komawa Gidansa a Aso Villa a Abuja

  • Bayan kusan shekara guda da kammala sabuwar fadar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima bai koma ciki ba
  • Rahotanni sun nuna cewa ana rade radin matsalolin tsaro ne suka haddasa jinkirin komawar mataimakin shugaban kasar
  • Hukumar raya birnin tarayya (FCTA) ta ce ta kammala aikin da aka dora mata kuma ta mika gidan ga fadar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bincike ya nuna cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, bai koma fadar da aka gina masa ba, duk da cewa an kammala ta kusan shekara guda da ta gabata.

An ce an kammala ginin ne a kan kudi kimanin Naira biliyan 15, inda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shi a ranar 7 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

Kashim Shettima
Gwamnatin tarayya ta gaza bude sabon gidan mataimakin shugaban kasa da ya lashe N15bn. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

A yayin da jaridar Daily Trust ta ziyarci wurin a ranar 31 ga watan Janairu, 2025, ba a ga wata alama ta amfani da gidan ba, sai dai wasu jami’an tsaro da ke bakin aiki a wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya hana Kashim Shettima komawa sabon gida?

Ana hasashen matsalolin tsaro na daya daga cikin dalilan da suka sa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, bai koma katafariyar fadar da aka gina masa ba a Abuja.

Wasu majiyoyi da suka yi magana da manema labarai sun ce wurin da aka gina fadar ba shi da tsaro sosai, don haka bai dace a zaunar da mataimakin shugaban kasa a ciki ba.

A cewar majiyoyin, matsalolin tsaron na iya zama dalilin da ya sa Shettima bai koma ciki ba har yanzu.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin gwamnati da ke tabbatar da ikirarin majiyoyin.

Kara karanta wannan

2027: Kashim Shettima ya fadi yadda ya ke mu'amalantar Atiku a bayan fage

Ba a samu karin bayani daga gwamnati ba

Da aka tuntubi kakakin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, domin jin ta bakinsa kan lamarin, ba a same shi ba.

Haka nan, majiyar da ke da alaka da fadar shugaban kasa ba ta bayar da cikakken bayani kan dalilin da ya sa Shettima bai koma sabuwar fadar ba.

Duk da haka, wani jami’i daga hukumar raya birnin tarayya (FCDA) ya bayyana cewa dukkanin ayyukan da aka dora wa hukumar sun kammala.

Jami’in, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce an mika aikin ga fadar shugaban kasa tun lokacin da aka kaddamar da shi a bara.

Ana jiran matakin da gwamnati za ta dauka

Yanzu haka, ana ci gaba da jiran matakin da gwamnatin tarayya za ta dauka kan sabuwar fadar mataimakin shugaban kasar.

Duk da cewa an kashe makudan kudi wajen gina wurin, har yanzu ba a tabbatar da ko Shettima zai koma cikinsa nan ba da jimawa ba ko a’a.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kano, gobara ta kashe dabbobi 78, ta lalata kayan abinci

A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin samun karin bayani daga bangaren gwamnati don jin ainihin dalilan da suka hana mataimakin shugaban kasa komawa sabon gidansa.

Har zuwa lokacin da za a fitar da wata sanarwa daga hukumomin gwamnati, lamarin na ci gaba da jan hankalin jama’a da ‘yan siyasa a Najeriya.

Kashim Shettima ya yi magana kan Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa matamakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce yana girmama Atiku Abubakar.

Sai dai duka da haka Kashim Shettima ya ce hakan ba zai hana shi buga siyasa a zaben 2027 idan har Atiku ya fito zai kara da jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng