Yadda Sojoji Suka Kashe 'Yan Ta'adda 27 tare da Kwato Makamai Masu Tarin Yawa

Yadda Sojoji Suka Kashe 'Yan Ta'adda 27 tare da Kwato Makamai Masu Tarin Yawa

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi bayani kan nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu a cikin mako guda a kasar nan
  • Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 27 tare da ceto mutane 44 da aka yi garkuwa da su
  • Manjo Janar Markus Kangye ya kuma bayyana cewa sojojin sun cafke ɓarayin fetur tare da ƙwato kayayyaki masu yawa a hannunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan ƴan ta'adda a cikin mako guda.

DHQ ta bayyana cewa sojojin masu aikin samar da tsaro, sun kashe ƴan ta’adda 27, sun cafke wasu 62, sannan sun ceto mutane 44 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi taron dangi kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Najeriya
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 27 a cikin mako guda Hoto: @ZagazolaMakama
Source: Twitter

Sojoji sun cafke ɓarayin man fetur

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Manjo Janar Markus Kangye ya ce tsakanin ranakun 30 ga watan Janairu da 7 ga watan Fabrairu, 2025, sojoji sun kama mutane 23 da ake zargi da satar man fetur tare da ƙwato kayayyakin sata da darajarsu ta kai N292,644,100.

Ya bayyana adadin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da, ɗanyen fetur lita 253,330, lita 42,000 na dizal da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, lita 5,100 na man fetur, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Yadda sojoji suka kashe ƴan ta'adda

  • Rundunar Operation Hadin Kai: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 18, sun kama 11, tare da ceto mutane 31 da aka sace.
  • Rundunar Operation Fasan Yamma: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda takwas, sun kama guda shida, tare da ceto mutane 55 da aka yi garkuwa da su.
  • Rundunar Operation Safe Haven: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda huɗu, sun ceto mutane 13 a yankin Arewa ta Tsakiya.
  • Rundunar Operation Delta Safe: Sojoji sun kama mutane 23 da ake zargi da satar man fetur, sun lalata haramtattun wuraren tace mai, tare da ƙwato makamai da alburusai.
  • Rundunar Operation Whirl Stroke: Sojoji sun kashe ɗan ta’adda ɗaya sannan sun kama mutane 30 da ake zargi da aikata ta’addanci.
  • Ayyuka a Kudu maso Gabas: Dakarun soji sun kama ƴan ta’adda biyar na IPOB/ESN, sun lalata nakiyoyi, sannan sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara

Manjo Janar Markus Kangye ya kuma bayyana cewa sojojin sun ƙwato makamai 61 da harsasai 1,584.

Jami'an tsaro na ƙoƙari

Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa jami'an tsaro na ƙoƙari sosai a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a faɗin Najeriya.

"Muna ganin irin nasarorin da suke samu kan ƴan ta'adda. Tabbas hakan abin a yaba ne. Dama abin da muke fata kenan su zage damtse wajen kawo ƙarshen ƴan ta'adda."

- Muhammad Auwal

Sojoji sun kashe hatsabibin ɗan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe hatsabibin ɗan bindiga, Kachalla Na Faranshi, a jihar Zamfara.

Sojojin sun samu gagarumar nasarar hallaka ɗan bindigan ne a wani samame da suka kai a dazukan Zurmi cikin ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng