Ramadan: Dan Majalisa Ya Jiƙa Yan Mazabarsa da Miliyoyin Naira, Ya ba Su Shawara

Ramadan: Dan Majalisa Ya Jiƙa Yan Mazabarsa da Miliyoyin Naira, Ya ba Su Shawara

  • Dan majalisar wakilai Abdussamad Dasuki ya bada tallafin Naira miliyan 100 domin azumin Ramadan ga mutanen mazabarsa a jihar Sakkwato
  • An kafa kwamitin mutum 35 da ke dauke da limamai da shugabanni domin rarraba kayan agaji ga al’ummar mazabar kafin Ramadan ya karaso
  • Dasuki ya bukaci jama’a su ci gaba da kyautatawa, yana mai cewa Ramadan wata dama ce ta sada zumunta da taimakon mabukata a cikin al’umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato, Abdussamad Dasuki ya yi abin alheri ga yan yankinsa.

Hon. Dasuki ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 domin azumin watan Ramadan ga jama’ar mazabarsa da ke jihar Sokoto.

Azumin Ramadan ya gabato, dan Majalisar ya yi rabon tallafi
Hon. Abdulsamad Dasuki ya ba tallafin N100m ga yan mazabarsa saboda Ramadan. Hoto: Abdulsamad Dasuki.
Asali: Facebook

Dan majalisa ya ba da tallafin Ramadan

Dasuki ya mikawa kwamitin mutum 35 domin sayen kayan tallafi da rarraba su, yana mai cewa hakan ya dace da halin tattalin arziki, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

'Dan majalisar ya ce yadda Ramadan ya gabato yana bukatar ba al'umma tallafi domin rage musu wahala.

“Ramadan yana gabatowa, kuma abin da muke yi yau shi ne tabbatar da cewa Musulmai a Kebbe/Tambuwal sun samu tallafi yayin azumin Ramadan."
“Muna son tabbatar da cewa an rarraba tallafin kafin Ramadan domin rage radadin rayuwa ga jama’a yayin wannan wata mai alfarma."

- Hon. Dasuki

Yadda aka kafa kwamitin rabon tallafin Ramadan

Hon. Dasuki ya ce kwamitin agajin Ramadan ya kunshi limamai da shugabanni a mazabar domin tabbatar da cewa kayan tallafin sun isa ga mabukata.

Kwamitin yana karkashin jagorancin Hon. Abubakar Sadiq Sanyinna, shugaban dattawan Tambuwal, tare da Hon. Adamu Haruna Kebbe a matsayin mataimaki.

Sakataren kwamitin shi ne Hon. Attahiru Danmadi, babban hadimin majalisa ga Hon. Dasuki, tare da shugabannin PDP na Kebbe da Tambuwal a cikin kwamitin.

Dasuki ya bukaci mutanen mazabar Kebbe/Tambuwal da su rungumi kyautatawa da taimakon juna domin karfafa hadin kai da jin kai a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Ya ce azumin Ramadan yana daga cikin shika-shikan addinin Musulunci, don haka yin ayyukan alheri da sadaka yana karfafa hadin kai da tausayi a cikin al’umma.

Ramadan: Sheikh Guruntum ya ba da shawara

Kun ji cewa malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ce yana da muhimmanci Musulmi masu gaba da juna su yi sulhu kafin shigowar Ramadan.

Malamin ya bayyana cewa husuma da gaba suna hana karɓar azumi, don haka yana da kyau a daidaita sabani kafin watan azumi ya kama.

Sheikh Guruntum ya jaddada muhimmancin ciyarwa a Ramadan, yana mai ishara da cewa ya kamata kowa ya yi iya kokarinsa wajen ciyarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.