"Shirin Gwamnati Ya Gaza, " Tsohon Gwamnan APC Ya Fito da Matsalolin Mulkin Tinubu

"Shirin Gwamnati Ya Gaza, " Tsohon Gwamnan APC Ya Fito da Matsalolin Mulkin Tinubu

  • Dr. John Kayode Fayemi ya ce aniyar shugaba Bola Tinubu kadai ba ta wadatar da nasara, dole a samar da tsare-tsaren da suka dace
  • Tsohon gwamnan ya ce matakan Tinubu sun haddasa tsadar rayuwa, ciki har da cire tallafin fetur da sauya tsarin musayar kuɗi
  • Fayemi ya ce dole ne shugabannin Najeriya su nemi gafarar ‘yan ƙasa saboda gazawar da su ka yi wajen cika alkawurran da su ka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja -Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce shugaba Bola Tinubu na da kyakkyawar aniya ga Najeriya, amma hakan kadai bai isa ya kawo canji ba.

Tsohon gwamnan ya ce dole ne gwamnatin Tinubu ta ƙara ingantaccen tsari na manufofi don haɗa shi da ƙwarewar jagoranci da ake da ita, domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi wa El Rufai wankin babban bargo, ya fadi wani sirrinsa

Tinubu
Kayode ya shawarci Tinubu a kan tattalin arziki Hoto: Kayode Fayemi/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa tsohon gwamnan na ganin duk da Tinubu ya ɗauki matakai masu tsauri da ya kamata a ɗauka tun tuni, akwai buƙatar a canja taku idan ana son inganta rayuwar jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Tsare-tsaren Tinubu sun jawo matsala,” Fayemi

The Cable ta wallafa cewa tsohon gwamnan Ekiti na ganin cewa tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu sun jawo ƙalubale da dama ga tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi abubuwa masu kyau da dama; dole ne mu amince da hakan. Ya nuna jarumtaka wajen ɗaukar wasu daga cikin matsanancin matakan da shugabannin baya suka ki ɗauka.”
"Amma sakamakon waɗannan matakan ya haddasa tsadar rayuwa mai tsanani. Cire tallafin fetur, haɗa kasuwar musayar kuɗi."

Fayemi: Aniyar Tinubu kadai ba ta isa ba

Kayode Fayemi ya bayyana cewa duk da Tinubu na da kyakkyawar aniya, hakan kadai bai isa ya magance matsalolin tattalin arzikin da ƙasar ke fama da su ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Tsohon gwamnan ya ce:

"Duk da yana da niyya mai kyau, amma hakan kadai bai isa a jagoranci ba; jajircewa da tsari mai nagarta su ne mabuɗin nasara.”
"Ko ana magana kan lamunin ɗalibai, ko ƙoƙarin murƙushe ta’addanci, rage rashin tsaro, gyaran manufofin haraji, ko kuma ƙara kuɗin shiga na tarayya; akwai wasu abubuwan da ke aiki, amma suna buƙatar haɗuwa wuri guda.”
"A nan ne tsari mai kyau na manufofi zai tafi tare da ƙwarewar jagoranci domin sauya labarin yadda ake tafiyar da al’amura. Wataƙila nan ne wurin da ya kamata mu ƙara mayar da hankali."

Fayemi ya shawarci shugabanni a Najeriya

Tsohon gwamnan ya kuma ce dole ne shugabannin ƙasa su nemi afuwar ‘yan Najeriya saboda sun kasa cika alkawurran da suka dauka a gare su.

Ya ce:

"Babu shakka, dole ne mu nemi gafarar al’ummar Najeriya. Ba mu samu nasarar aiwatar da duk alkawurran da muka ɗauka ba, ba wai saboda mun kasa ko rashin ƙwarewa ba, amma saboda wasu matsalolin tsarin gwamnati da suka sa abubuwa suka fi wahala."

Kara karanta wannan

"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala

"Dole ne mu daidaita yadda muke tafiyar da al’amura, domin idan ba mu yi hakan ba, haɗarin da muke fuskanta ya fi ribar da za mu samu."

Tinubu ya yi kora a jami'o'in tarayya

A baya, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga mukaminta na shugabar Jami'ar Abuja, ya nada Farfesa Lar Patricia Manko a sabuwar shugaba na watanni shida.

A Jami'ar Najeriya Nsukka (UNN), ya sauke Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga mukaminsa na mukaddashin shugabar jami'ar, ya nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin sabon shuganta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.