El Rufa'i Ya Dira a kan Uba Sani saboda Tsare Tsofaffin Jami'an Gwamnatin Kaduna
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da katsalandan a shari’ar cin hanci da ake yi wa makusantansa
- El Rufa'i ya na zargin cewa gwamnati mai-ci a Kaduna, da shi kansa gwamna Uba sun shiga maganar wajen hana a bada belin hadimansa
- Tsohon gwamnan ya koka kan yadda ake binciken wasu, amma wasu sun tsira saboda matsayinsu a gwamnati mai-ci a jiha ko tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi magajinsa, Gwamna Uba Sani, da gwamnatin jihar da katsalandan a shari’ar cin hanci da ake yi wa wasu daga cikin hadimansa.
Ya kara da zargim gwamnan da hana a sako su daga gidan yari don dalilan siyasa, kuma ya na ganin shari’un sun fara daukar salo na siyasa maimakon a bar su a tafarkin shari’a na doka.

Kara karanta wannan
Jami'an gwamnatin El Rufa'i sun goyi bayansa, an zargi Uba Sani da bita da kullin siyasa

Asali: Facebook
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, El-Rufai ya nuna damuwa kan yadda shari’un Bashir Sai’du da Jimi Lawal, wadanda suka yi aiki a gwamnatinsa, ke tafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC na shari’a da makusantan El-Rufai
Daily Trust ta wallafa cewa hadiman El-Rufai biyu na fuskantar tuhuma kan zarge-zargen cin hanci da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar a kansu a jihar.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da belin Jimi Lawal, wanda ya kasance babban mashawarci a gwamnatin El-Rufai.
An kuma ba da belin wasu mutum uku a ranar 21 ga Janairu, 2025, a shari'ar da ake tuhumarsu da zamba da wasu laifuka daban-daban.
El-Rufai na zargin gwamnatin Uba Sani
Tsohon gwamnan Kaduna ya zargi gwamnati mai ci da yi wa makusantansa da su ka yi aiki a gwamnatinsa farautar siyasa,.
Ya yi zargin cewa amma jami'an gwamnatinsa da suka sauya sheka zuwa sabuwar gwamnati mai ci ba su da irin wannan matsala ta tuhumarsu da zamba.

Kara karanta wannan
"Ba za mu bari ba," Lauya, Abba Hikima ya je inda ake harbe mutane wajen rusau a Kano
El Rufa'i ya ce:
"Domin fahimtar abin da ke faruwa, dole ne a gane cewa tun farkon shekarar 2024, an rika gayyato da tuhumar mutanen da su ka yi aiki a gwamnatin El-Rufai ta hanyoyin hukumomin yaki da cin hanci. Amma mafi yawan wadanda aka sa a gaba su ne wadanda aka sani da kasancewa tare da El-Rufai duk da ya bar mulki.
"Wasu da dama sun tsira daga bincike sakamakon matsayinsu a gwamnatin Gwamna Uba Sani ta Kaduna ko kuma a matakin kasa. Wannan tsarin da ya keɓance wasu a binciken na jefa shakku kan adalcin shari’ar.
"Sharri ake yi masa," Tsofaffin jami'an gwamnatin El Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa tsofaffin jami'an gwamnatin Kaduna sun musanta zargin cin hanci da rashawa da ake yi musu a gwamnatin da Nasir El Rufa'i ya jagoranta.
Sun jaddada cewa zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamna Nasir El-Rufai ba su da tushe, kuma ana zargin gwamnatin Uba Sani ta na yi su haka ne don bata masa suna a idon jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng