Noma: Sanata Barau Zai Raba Naira Biliyan 2.79 ga Matasa a Jihohin Arewa
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya fitar da shirin tallafawa matasa 558 domin su zama masu dogaro da kai
- Rahotani sun tabbatar da cewa kowane matashi daga cikin wadanda za a zaba zai samu tallafin Naira miliyan 5 domin fara noma
- Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa shirin zai mayar da hankali a kan noma masara da shinkafa domin bunkasa samar da abinci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana shirin da ya fitar domin tallafawa matasa 558 a Arewa maso Yamma.
Sanata Barau ya bayyana cewa shirin zai bada tallafi ga matasa uku daga kowanne daga cikin kananan hukumomi 186 na jihohin Arewa maso yamma.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai a kan shirin ne a cikin wani sako da Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin na da nufin dawo da martabar noma a Arewa ta Yamma da kuma tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.
Sanata Barau zai tallafawa matasa 558
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya ya fitar da shirin tallafawa matasa da jari domin yaki da fatara da dogaro da kai a Arewa maso Yamma.
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa kowanne daga cikin matasan da aka zaba zai karɓi Naira miliyan 5 domin zuba jari a harkar noma.
Barau Jibrin ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen farfado da harkar noma a yankin, inda aka mayar da hankali kan noma shinkafa da masara.
Ya kara da cewa hakan zai rage tsadar kayan abinci kuma ya inganta samar da isasshen abinci ga al'umma.

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
"Babu wata kasa da za ta iya ci gaba ba tare da ta samar da wadataccen abinci ga al’ummarta ba.
"Abinci ne ginshikin tsaro, ba wai kawai ga mutum ba, har ma ga gidaje, kananan hukumomi, jihohi da kasa baki daya,"
- Sanata Barau Jibrin
Mutanen da za su amfana a jihohi
Sanata Barau ya bayyana cewa an raba adadin matasan da za su ci gajiyar shirin kamar haka:
- Kaduna – 69
- Kano – 132
- Kebbi – 63
- Katsina – 102
- Jigawa - 81
- Sokoto – 69
- Zamfara – 42
Ya ce matasan da aka zaba za a horas da su kan ingantattun hanyoyin noma tare da ba su kayan aiki da jari domin su iya gudanar da aikin su cikin nasara, inda za a kashe Naira biliyan 2.79.
Alakar shirin da karancin abinci
A cewar Sanata Barau an tsara shirin ne domin yin amfani da filayen noma masu yawa da ke yankin Arewa maso Yamma, tare da tabbatar da cewa yankin ya dawo da martabarsa.
"A shekarar 2023, Najeriya ta samar da tan miliyan 8.9 na shinkafa, wanda shine mafi yawa tun shekarar 2010.
"Amma har yanzu wannan adadi bai wadatar ba saboda yawan jama'a na karuwa. Saboda haka, shirin zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta noman shinkafa da masara,"
Sanata Barau ya bayyana cewa gidauniyarsa tana hadin gwiwa da wata babbar cibiyar hada-hadar kudi domin aiwatar da shirin.
Haka zalika ya ce tuni an kammala shirye-shiryen kaddamar da shirin a watan Afrilu na wannan shekarar.
Za a farfado da noma a Nasarawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Nasarawa ya bayyana aniyarsa ta bunkasa harkar noma a jihar a damuna mai kamawa.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa yana shirye shiryen noma dukkan filayen jihar yayin wata ziyara da ya kai kasar China.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng