'Na Yi Kokari': Buhari Ya Jero Bangarorin da Ya Kawo Sauyi a Mulkinsa, an Yaba Masa

'Na Yi Kokari': Buhari Ya Jero Bangarorin da Ya Kawo Sauyi a Mulkinsa, an Yaba Masa

  • Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bangarorin da ya kawo sauyin yayin da yake mulkin Najeriya a zamaninsa
  • Buhari ya tabbatar da cewa a ɓangaren tsaro da tattalin arzikin Najeriya sun inganta sosai a lokacin mulkinsa na tsawon shekaru takwas
  • Dattijon ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan da suka magance matsalolin tattalin arziki da ta’addanci da suka addabi kasar kafin hawansa mulki a 2015
  • Shugaban ‘yan jaridu na Katsina, Yusuf Ibrahim-Jargaba, ya jinjinawa Buhari bisa jajircewarsa wajen dakile matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Katsina - Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya kawo ci gaba a wasu ɓangarori a Najeriya.

Buhari ya tabbatar da cewa tsaro da tattalin arzikin Najeriya sun inganta sosai a lokacin mulkinsa na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan

"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu

Buhari ya bugi kirji kan salon shugabancinsa
Muhammadu Buhari ya tabbatar da inganta tsaro da tattalin arziki a mulkinsa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

'Yadda na inganta tsaro da tattalin arziki'- Buhari

Buhari ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina yayin da ya karɓi bakuncin mambobin kungiyar ‘yan jarida, cewar Thisday.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar ya tuna cewa kafin zuwansa, Najeriya na fama da matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.

Amma da zuwansa, gwamnatinsa ta magance wadannan tarun matsaloli yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa tsare-tsaren da gwamnatinsa ta aiwatar sun taimaka wajen magance matsalolin da ya gada daga gwamnatocin da suka gabace shi.

Buhari, wanda ya yi magana da Hausa, ya ce:

“Tsaro da tattalin arziki sun inganta sosai a Najeriya karkashin mulkina fiye da yadda muka tarar a 2015.”

Buhari ya fadi kalubale da shugabanni ke fuskanta

Buhari ya ce sai wadanda ke cikin gwamnati ne ke fahimtar matsalolin mulki, yana mai cewa shugabanni kan fuskanci matsaloli wurin aiwatar da manufofi.

Tun da farko, Shugaban kungiyar ‘yan jarida na Katsina, Yusuf Ibrahim-Jargaba, ya jinjinawa Buhari bisa kokarinsa na yaki da ta’addanci da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sarki ya jefa kansa a matsala, Gwamna ya dakatar da basarake kan cin zarafin dattijo

Ibrahim-Jargaba ya ce, duk da ra’ayoyi daban-daban, Buhari ya dage wajen tabbatar da ci gaba da hadin kan kasar Najeriya a lokacin shugabancinsa.

Dan Bello ya gina rijiyar burtsatse a Katsina

Kun ji cewa sanannen mai wasan barkwanci a kafafen sada zumunta, Dan Bello, ya gina rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a ƙauyuka biyu na Katsina .

Rijiyoyin sun ci kimanin kuɗi har N4.3m kuma ta taimaka wajen kawar da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha da al’ummar jihar suka dade suna fama da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.