Sarki Ya Jawo Wa Kansa Wahala, An Tasa Ƙeyar Mai Martaba zuwa Gidan Gyaran Hali

Sarki Ya Jawo Wa Kansa Wahala, An Tasa Ƙeyar Mai Martaba zuwa Gidan Gyaran Hali

  • Rahotanni sun nuna cewa dakataccen sarkin Orile Ifo a jihar Ogun wanda ake tuhuma da cin zarfi ya gaza cika sharuɗɗan beli
  • Jami'an tsaro sun tasa keyar basaraken, Oba Abdulsemiu Ogunjobi zuwa gidan gyaran halin Ilaro domin ajiye shi zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗa
  • Ƴan sanda sun cafke sarkin tare da gurfanar da shi a gaban kotun bayan wani bidiyo ya nuna yadda ya ci mutuncin wani dattijo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - An tasa keyar dakataccen sarkin gargajiya na Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi zuwa gidan gyaran hali a jihar Ogun.

Jami'an tsaro sun tasa shi zuwa gidan gyaran halin ne saboda ya gaza cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi ranar Talata

Taswirar Ogun.
Duk da kotu ta ba da belinsa, an garkame basaraken Ogun a gidan gyaran hali Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahoton The Nation ya nuna cewa tun farko rundunar ‘yan sandan Ogun ta gurfanar da basaraken a gaban kotun majistire da ke Ifo a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Majalisar amintattun PDP ta shiga taron gaggawa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da ya sa aka tura sarkin gidan yari

Ƴan sanda sun kama sarkin tare da gurfanar da shi ne kan wani faifan bidiyo da ya yadu wanda aka gan shi yana cin zarafin wani mutum mai shekara 73, Abraham Areola.

A cewar takardar tuhumar mai lamba (MH2b8c/2025), an zargi Oba Ogunjobi da laifukan hada baki, cin zarafi da aikata abu da zai iya haddasa tashin hankali.

Jerin tuhume-tuhume 3 da ake yi masa

A takardar shigar da ƙara, rundunar ƴan sanda ta bayyana tuhume-tuhume uku da take wa sarkin wanda suka haɗa da:

1. Hada baki:

“Cewa kai, Abdul-Semiu, da wasu da ba a kama ba, a ranar 21 ga Janairu, 2025, da misalin karfe 11:00 na safe, a titin Sojuolu, yankin Ifo, kun hadu kun aikata laifin cin zarafi da ka iya haddasa tashin hankali, hakan ya sabawa sashe na 517 na dokar laifuka ta jihar Ogun, 2006.”

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a makarantar allo, an samu asarar rayukan dalibai

2. Cin zarafi:

“Cewa kai, Abdul-Semiu, da wasu da ba a kama ba, a wannan rana da lokaci da aka ambata, ka ci zarafin Areola Abraham ta hanyar marinsa a fuska da kunne, wanda hakan ya sabawa sashe na 351 na dokar laifuka ta jihar Ogun, 2006.”

3. Haifar da tashin hankali:

“Cewa kai, Abdul-Semiu, da wasu da ba a kama ba, ka aikata abu da zai iya haddasa tashin hankali ta hanyar tilastawa Areola Abraham durkusawa sannan ka ci mutuncinsa a bainar jama’a, wanda hakan ya sabawa sashe na 249 (d) na dokar laifuka ta jihar Ogun, 2006.”

Basaraken ya musanta aikata laifuffukan

Sai dai Oba Ogunjobi ya musanta dukkan tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a F. A. Iroko, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Kotu ta ba shi beli a kan kudi Naira miliyan 5 tare da sharaɗin kawo waɗanda za su tsaya masa mutum biyu da ke zaune a yankin da kotun take zama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun yi awon gaba da fasinjoji zuwa daji

Sakamakon rashin cika sharuɗɗan belin, an tasa basaraken da ya ci mutuncin dattijo zuwa gidan gyaran halin Ilaro da ke jihar Ogun.

Gwamnan Ogun ya dakatar da basarake

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya dakatar da sarkin Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi na tsawon watanni shida.

Bayan dakatar da shi, an kuma ƙwace duk wata shaida da ke nuna shi sarki ne har sai an kammala bincike da shari'a kan tuhume-tuhumen da ke kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262