Oluremi Tinubu Ta Ji Kan Mutanen Neja, Ta ba da Tallafin N100m
- Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta ba da gudummawar Naira miliyan 100 ga wadanda gobarar tankar mai ta shafa a jihar Neja
- Oluremi Tinubu ta bayyana cewa manufar gudummawar ita ce tallafa wa iyalai kusan 70, inda kowanne zai samu akalla Naira miliyan daya
- A nasa bangaren, Mai girma gwamna Umaru Bago ya ce ziyarar matar shugaban kasa za ta karfafa gwiwa ga iyalan da gobarar ta shafa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta ba da gudummawar Naira miliyan 100 ga wadanda gobarar tankar mai ta shafa a jihar Neja.
Matar shugaban kasa ta sanar da wannan gudummawa ne yayin da ta kai ziyarar jaje zuwa gidan gwamnatin jihar a Minna, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan
Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa

Asali: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa Oluremi Tinubu ta je jihar ne domin yin jaje ga Gwamna Umaru Bago kan mummunar gobarar tankar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 80.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar ta afku ne a ranar 18 ga watan Janairu a unguwar Dikko da ke karamar hukumar Gurara ta jihar, inda ta lalata dukiyoyi da dama tare da jikkata mazauna yankin da dama.
Neja: Oluremi Tinubu ta ba da gudunmawa
Jaridar The Nation ta wallafa cewa matar shugaban kasa ta bayyana cewa manufar wannan gudummawa ita ce tallafa wa iyalan da gobarar ta shafa.
Ta ce:
“Muna shirin tallafa wa iyalai kusan 70 ta hannun matar gwamna, Hajiya Fatima Bago, inda kowanne iyali zai samu Naira miliyan 1 domin taimaka masu.
"Sauran kudin kuma za a yi amfani da su wajen daukar nauyin wasu karin bukatu kamar kayan abinci."
Oluremi Tinubu ta yabi kokarin gwamnatin Neja
Oluremi Tinubu ta yaba wa kokarin Gwamna Umaru Bago wajen taimaka wa iyalan da gobarar ta shafa da kuma nasarorin da ya samu a fannin noma a jihar.
A bangarensa, gwamna Bago ya nuna godiyarsa ga matar shugaban kasa bisa ziyarar da ta kawo jihar domin jaje ga al’umma bisa iftila’in da ya faru.
Gwamnatin Neja ta gode wa Oluremi Tinubu
Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa wannan ziyarar ta zama karfafa gwiwa ga iyalan da gobarar ta shafa.
Ya ce:
"Ziyarar za ta karfafa wa mutanen da gobarar tankar a unguwar Dikko ta shafa gwiwa. Mun gode da gudummawar da matar shugaban kasa ta bayar ta hanyar bada Naira miliyan 100 domin tallafa wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.”
Oluremi Tinubu ta tallafa wa mazauna Borno
A wani labarin, kun ji cewa Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta nuna alhininta kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno, inda ta ba da gudummawar Naira miliyan 500.
Oluremi Tinubu, wacce ta samu wakilcin Hajiya Nana Kashim Shettima, uwargidan mataimakin shugaban kasa, ta bayyana damuwarta kan wannan mummunar ambaliyar ruwa tare da yin jaje.
Gwamna Zulum ya nuna godiyarsa ga uwargidan shugaban kasa da tawagarta bisa wannan taimako da zai taimaka wajen saukaka wa mutanen da ambaliyar ta shafa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng