"Kudi Fitina ne," Sheikh Dutsen Tanshi Ya Magantu a kan Dambarwar Iyalan Albani

"Kudi Fitina ne," Sheikh Dutsen Tanshi Ya Magantu a kan Dambarwar Iyalan Albani

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, ya bayyana ra'ayinsa a kan dambarwar iyalan Auwal Albani
  • Sheikh Dutsen Tanshi ya cewa maganar iyalan Sheikh Muhammad Auwal Albani ba ya rasa nasaba da wakafin da marigayin ya bari
  • Malamin ya bukaci a gudanar da bincike cikin natsuwa a kan dukkannin koken da iyalan Sheikh Albani suka gabatar ga duniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya bayyana fatan batun iyalan Sheikh Muhammad Auwal Adam ba a kan wakafin marigayin ba ne.

Babban malamin ya yi zargin cewa makarantar da Sheikh Auwal Albani ya bari ce ta ke tsone wa jama'a ido, har ta kai ga ana samun bullar abubuwa marasa dadi.

Kara karanta wannan

"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu

Tanshi
Sheikh Dutsen Tanshi ya tofa albarkin bakinsa kan dambarwar iyalan Albani Hoto: Ibrahim Aminu Rimin Kebe/IBee As-salafiy
Asali: Facebook

A wata hirar Sheikh Dutsen Tanshi da aka wallafa a shafin Facebook na DawaatulHaq, malamin ya ce Sheikh Muhammad Auwal ya na da 'yancin ya yi wakafi da dukiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wakafi ya halatta," Sheikh Dutsen Tanshi

Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya bayyana cewa addinin musulunci ya sahale wa bayin Allah su yi wakafi da dukiyar da su ka mallaka domin neman yardar Allah SWT.

Sheikh Dutsen Tanshi ya ce:

"Na fara da farko da hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ke cewa idan 'dan adam ya mutu, ayyukansu duk sun yanke, sai abubuwa uku su ne ba sa yanke wa.

Ya bayyana cewa daga cikin wadannan abubuwa uku akwai sadakatul jariya, wanda ke nufin wakafi, sai 'da na gari da zai ci gaba da yi wa mamaci addu'a da ilimi da za a amfana da shi.

Fatan Dutsen Tanshi ga iyalan Albani

Babban malamin nan, Sheikh Dutsen Tanshi ya bayyana fatan cewa iyalan Albani ba su bijiro da maganganun cewa Darul Hadith sun ki taimakonsu ne saboda son dukiya ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala ya rasu a Filato

Ya ce dukiya fitina ce da ke iya hallaka dan adam, kuma ya na daya daga cikin abubuwan da ke jawo rashin jituwa a tsakanin mutane.

A hirar ya ba da misali da makarantarsa da ya gina a Bauchi, ya ce ko a watan jiya sai da ya yi amfani da kudin aljihunsa wajen biyan albashi.

Saboda haka ne ya yi kira ga masu kwallafa rai da Darul Hadith su ji tsoron Allah SWT.

Malamin ya kara da bayyana cewa:

"Taimaka masu abu ne mai kyawu, kuma bai shafi maganar wakafi da shi Sheikh Muhammad Auwal Albani ya yi ba. Bai shafe shi ba.
Amma mu dai abin da mu ke guje wa, kar ya mayar da su 'yan kwara. Ka da kuma ya sa don wannan dalili ya sa aka taso da wannan matsala.

Sheikh Dutsen Tanshi ya kara da cewa ya kamata a bi sannu a hankali wajen gudanar da bincike a kan dukkanin koken da iyalan Albani su ka yi domin daukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Kaduna: Musulunci ya samu karuwa da Kirista ta karbi kalmar shahada, an shawarce ta

Dutsen Tanshi ya kira ga gwamnatin Bauchi

A baya, mun ruwaito cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sake duba bayan yanka filin idi.

Malamin ya bayyana damuwarsa kan yadda aka yanka filin da shi da mabiyansa ke amfani da shi wajen sallar idi, inda ya ce wannan mataki na iya haifar da rashin jituwa tsakanin jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel