Gwamanti Ta Fara Karbar Haraji daga Direbobin da Ke Bin Hanyar Abuja zuwa Makurdi

Gwamanti Ta Fara Karbar Haraji daga Direbobin da Ke Bin Hanyar Abuja zuwa Makurdi

  • Gwamnatin tarayya ta fara karbar haraji daga hannun direbobin da ke bin hanyar Abuja-Akwanga-Lafia-Makurdi daga ranar Talata
  • An rahoto cewa kananan motoci za su biya N500 yayin da manyan motoci za su biya N1600 a duk lokacin da suke je wucewa ta hanyar
  • Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi bayanin dalilin gwamnati na fara karbar harajin da kuma abin da za a yi kudaden idan an tara su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Gwamnatin tarayya ta fara aikin karbar haraji a kan babbar hanyar Abuja–Akwanga–Lafia–Makurdi daga ranar Talata, 4 ga watan Janairun 2025.

An rahoto cewa, gwamnati za ta yi amfani da kudin da aka tara domin biyan bashin dala miliyan 460.8 da ta karbo daga bankin China Exim.

Ministan ayyuka ya yi bayani game da karbar haraji daga dirbobi a hanyar Abuja-Makurdi
David Umahi ya fadi dalilin gwamnatin tarayya na fara karbar haraji daga direbobi a hanyar Abuja-Makurdi. Hoto: @realdaveumahi
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa cewa direbobi za su fara biyan haraji daga N500 ga kananan motoci har zuwa N1,600 ga manyan motoci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira biliyan 885 don ayyukan tituna 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara karbar haraji a hanyar Abuja-Makurdi

Sai dai kuma, gwamnatin tarayyar ta ce motocin 'yan sanda da na sojoji ba za su biya kudin harajin ba domin saukaka ayyukansu, inji rahoton Daily Trust.

Rahoton ya nuna cewa an raba shingen karbar harajin zuwa sassa hudu: Hanyar zuwa Keffi, hanyar zuwa Akwanga, hanyar zuwa Lafia da hanyar zuwa Makurdi.

An gyara tara da inganta hanyar mai nisan kilomita 227.2 ta hanyar lamunin bashi daga bankin China Exim wanda gwamnatin da ta shude ta karbo.

Minista ya magantu kan dalilin karbar harajin

A cikin yarjejeniyar lamunin, gwamnatin tarayya ta amince da karbar haraji a wannan hanya bayan kammala aikin, inda za a biya bashin da kudin da aka samu daga harajin.

A wajen kaddamar da aikin karbar haraji a shingen karbar harajin na Garaku da ke jihar Nasarawa, Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi karin bayani.

Kara karanta wannan

Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa

David Umahi ya tabbatar da cewa gwamnati za ta kula da dukkanin hanyoyin tarayya ta hanyar samar da kudade daga hanyoyi daban daban.

Da ya samu wakilcin karamin ministan ayyuka, Bello Goronyo, Umahi ya ce za a yi amfani da wani kaso na kudin harajin da ake karba daga direbobi wajen kula da hanyoyin tarayya.

Direbobi za su biya haraji a hanyar Abuja-Keffi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya kaddamar da kwamitin aiwatar da tsarin karbar haraji a kan hanyar Abuja zuwa Keffi.

Umahi ya ce sabon tsarin karbar harajin wani mataki ne na gwamnati domin inganta titunan kasar yayin da za a mayar da titin Keffi-Akwanga-Makurdi zuwa hannu biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.