'Yan Sanda Sun Yi wa 'Yan Bindiga Jina Jina bayan Gwabza Fada a Daji

'Yan Sanda Sun Yi wa 'Yan Bindiga Jina Jina bayan Gwabza Fada a Daji

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tare da haɗin gwiwar 'yan farauta sun kashe ‘yan bindiga biyu a wani samame a dajin Madan
  • An kwato bindiga kirar AK-49 da harsasai guda tara yayin wannan samame da aka gudanar a yankin Gwana bayan an gwabza fada
  • Rundunar ‘yan sanda ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaki da ‘yan bindiga tare da buƙatar haɗin kan al’umma domin inganta tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tare da haɗin gwiwar ƙungiyar 'yan farauta sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga biyu a wani samame da suka kai da sassafe a daji.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a dajin Madan da ke yankin Gwana, kusa da iyakokin jihohin Taraba, Filato da Gombe.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: An kama 'yan kasashen waje 165 da shirin kulla makirci a Najeriya

Bauchi
'Yan sanda sun kwato makamai bayan kashe 'yan bindiga a Bauchi. Nigeria Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ne ta fitar da rahoto a Facebook kan yadda aka gwabza fada tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'addar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar 4 ga Fabrairu, 2025.

"Wannan samame da aka shirya tare da haɗin gwiwar 'yan farauta ya haifar da gagarumar nasara inda aka kashe ‘yan bindiga biyu.
"An yi jina jina ga wasu 'yan bindigar kafin su tsere zuwa dazukan da ke makwabtaka da wajen,"

- CSP Ahmed Mohammed Wakil

Yadda aka kai samame ga 'yan bindiga

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa jami’anta a Alkaleri tare da 'yan farauta sun gudanar da sintiri a dajin Madan, wanda aka dade ana zargin cewa mafakar ‘yan ta’adda ne.

"Mun yi amfani da sahihan bayanan sirri da haɗin kan al’umma wajen kai farmakin
"Mun ci karo da wasu daga cikin ‘yan bindigar yayin sintirin da muke yi, inda aka yi musayar wuta da su, hakan ya kai ga kashe guda biyu a cikinsu,"

Kara karanta wannan

An koma ruwa: Hatsabibin dan bindiga da aka sako daga Nijar ya dawo Katsina

- CSP Wakil

Bayan kammala samamen, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK-49 da harsasai guda tara, alamu da ke nuna cewa ‘yan bindigar na shirin gudanar da ta’addanci a yankin.

'Yan sanda za su cigaba da kokari

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaki da duk wani nau’in laifi a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za ta ba wa ‘yan ta’adda damar samun mafaka ba.

Punch ta rahoto cewa CSP Wakil ya ce nasarar wata shaida ce ta jajircewar jami’an da goyon bayan al’umma wajen yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

'Yan Sanda: 'Mun kama bakin haure a Kebbi'

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama mutane 165 da ake zargi sun shigo Najeriya domin ta da zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna: Bayan El Rufa'i, Ashiru Kudan ya yi rubdugu ga Uba Sani

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa an kama mutanen ne a Birnin Kebbi kuma sun fito ne daga kasashe daban daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel