"Ba Wanda Ya Fi Karfin Doka": Gwamnan CBN da Wasu Ƙusoshin Gwamnatin Tinubu Sun Shiga Matsala

"Ba Wanda Ya Fi Karfin Doka": Gwamnan CBN da Wasu Ƙusoshin Gwamnatin Tinubu Sun Shiga Matsala

  • Majalisar Dattawa ta yi barazanar ba da umarnin cafke manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya kan ƙin amsa gayyatar da ta aika masu
  • Daga cikin waɗanda ke fuskantar kamen har da gwamnan CBN, Sufetan Ƴan sanda, shugaban FIRS da wasu shugabannin hukumomi
  • Kwamitin kula da asusun gwamnati a Majalisar dattawa ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka da har za a gayyace shi kuma ya ƙi zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bayyana shirinta na bayar da umarnin kama wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya da ke ƙoƙarin take doka.

Majalisar ta yi barazanar ba da umarnin kama manyan ƙusoshin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ne saboda sun ki amsa gayyatar da ta aika masu.

Majalisar dattawa.
Majalisar Dattawa ta yi barazanar sa a kama manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya Hoto: Nigeria Senate
Asali: Facebook

Gwamnan CBN da sauran ƙusoshin da za a kama

Kara karanta wannan

Alau: Gwamnatin Tinubu ta amince da aikin N80bn a Borno, ta fadi lokacin farawa

The Nation ta ce waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Sufeto-Janar na ‘Yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, Gwamnan Babban Banki (CBN) Yemi Cardoso, da Shugaban Kamfanin Man Fetur (NNPCL) Mele Kyari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran da ke fuskantar barazanar kamawa sun hada da Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS), Zacch Adedeji, da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, da wasu shugabanni na hukumomin gwamnati.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da Kwamitin Kula Asusun gwamnati na Majalisar Dattawa ya bukaci su bayyana gabansa domin kare kansu kan binciken da Ofishin Audita-Janar na Tarayya (AuGF) ya gudanar.

Dalilin barazanar kama ƙusoshin gwamnati

Shugaban kwamitin, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, ya ce shugabannin hukumomin da ake tuhuma sun ki amsa gayyatar Majalisar fiye da sau takwas.

Ya ce:

"Babu wanda ya fi ƙarin doka a Najeriya, idan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai iya zuwa Majalisa don gabatar da kasafin kudi, me ya sa waɗanda ya nada za su yi tunanin sun fi ƙarfin su bayyana?"

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Sanata Wadada ya kara da cewa daga yanzu, duk wanda aka gayyata kuma ya ki bayyana, Majalisar za ta fitar da umarnin kama shi.

Sannan ya ƙara da cewa Majalisar za ta bukaci shugaban kasa ya sallame shi daga mukaminsa.

Abin da ya sa Majalisa ta gayyace su

Kwamitin ya kuma bayyana cewa:

  • Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ya ki amsa gayyata sau takwas, tare da kin bada wata hujja ko amsa daga ofishinsa.
  • Shugaban NNPCL, Mele Kyari, bai taba bayyana gaban kwamitin ba, kuma amsoshin da ƙamfanin NNPCL ke bayarwa ba su da inganci.
  • Akwai biliyoyin Naira da ake bukatar Hukumar Kwastam (NCS) ta bayyana yadda aka sarrafa su.
  • Babban Bankin CBN ya kaucewa gayyatar Majalisa dangane da batun Ways and Means, wato bashi da gwamnatin tarayya ke ci daga bankin ba tare da izinin Majalisa ba.

An ji Wadada ya jaddada cewa duk wani jami’in gwamnati da ya gaza bayyana gaban kwamitin zai fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

Majalisar ta kuma yi barazanar cewa za ta bukaci Shugaban kasa ya tsige su daga mukamansu domin ba su goyon bayan manufarsa ta "Renewed Hope Agenda."

Majalisa za ta dawo da kudirin haraji

A wani labarin, kun ji cewa Majasar tarayya za ta dawo daga hutu kuma ana a ran za ta karya da kudirin harajin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Kudirin dai ya tayar da ƙura tun bayan gabatar da shi a Majalisa amma daga baya wasu daga cikin masu sukar dokar sun janye kalamansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262