Fitaccen Ɗan Kasuwa a Arewa, Albabello Ya Kwanta Dama, Manyan Kasa Sun Halarci Jana'iza

Fitaccen Ɗan Kasuwa a Arewa, Albabello Ya Kwanta Dama, Manyan Kasa Sun Halarci Jana'iza

  • An shiga alhini a Birnin Zaria bayan sanar da rasuwar fitaccen dan kasuwa, Alhaji Bala Albabello a farkon makon nan
  • Da safiyar yau Talata 4 ga watan Janairun 2025 aka yi jana’izar marigayin wanda shahararren ɗan kasuwa a Zaria
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ta rasu ne a jiya Litinin 3 ga watan Janairun 2025 bayan gajeruwar jinya
  • Babban Limamin Zazzau, Liman Dalhatu Kasimu ne ya jagoranci sallar jana’iza, tare da wakilan Sarkin Zazzau, karkashin jagorancin Wazirin Zazzau

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Zaria, Kaduna - Ana cikin jimamin rashin fitaccen dan kasuwa a birnin Zaria da ke jihar Kaduna, Alhaji Bala Albabello.

Rahotanni sun ce an yi sallar jana'izar marigayin da safiyar yau Talata wanda ya rasu jiya da yamma bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da ministoci da manyan kusoshin gwamnati a Abuja

An yi jana'izar fitaccen dan kasuwa a Arewacin Najeriya
Fitaccen ɗan kasuwa, Albabello ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Zazzau Emirate.
Source: Facebook

An yi jana'izar fitaccen dan kasuwa, Albabello

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Masarautar Zazzau ta wallafa a shafinta na Facebook.

Liman Dalhatu Kasimu, babban Limamin Zazzau ne ya jagoranci sallar jana’iza, yayin da Wazirin Zazzau ya jagoranci tawagar wakilan Sarkin Zazzau.

Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharazu da Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Injiniya Ahmed Mohammed Jamil duk sun halarci jana'izar.

Fitaccen 'dan kasuwan da yake kasuwanci a Zariya, ya fito ne daga yankin na Karaye a jihar Kano.

Manyan mutane da suka halarci jana'izar a Zaria

“Da safiyar yau aka gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Bala Albabello, shahararren ɗan kasuwa a Birnin Zaria, wanda ya rasu da yammacin jiya Litinin bayan gajeruwar jinya.
"Babban Limamin Zazzau, Dalhatu Kasimu, ne ya jagoranci sallar jana’izar, yayin da Wazirin Zazzau, Khadi Muhammadu Inuwa Aminu, MON, ya jagoranci tawagar wakilan Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, a wajen jana’izar.

Kara karanta wannan

"Ko ya musulunta ne?": Sanata ya ba mutane mamaki, ya yi sallah tare da musulmi

"Haka nan, Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharazu, da Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Injiniya Ahmed Mohammed Jamil, tare da dimbin jama’a, sun halarta, Allah Ya jikansa da rahama, amin."

- Cewar sanarwar

Sultan ya jajanta da rasuwar malamin Musulunci

A baya, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi ta’aziyya ga Musulmai da Kiristoci kan mutuwar Qamardeen Ajala da Injiniya Sunday Makinde.

Mutuwar Ajala, sanannen malami kuma mai gabatar da shirye-shiryen talbijin, ta faru tsakanin magariba da isha, yayin da Makinde ya rasu ranar Juma’a, 24 ga watan Janairun 2025.

Sarkin ya yaba da gudunmuwar marigayin Ajala wajen yada addini da ayyukan hajji inda ya yi masa addu'ar Allah ya yi masa rahama ya gafarta masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.