Sojoji Sun Kama Motar Makamai da ake Zargi za a Mika ga 'Yan Bindiga
- Rundunar sojojin Operation Safe Haven (OPSH) ta kama wani da ake zargin dillalin makamai ne a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato
- Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun ƙwato bindigogi iri daban-daban da alburusai da dama daga hannun wanda ake zargin a cikin wata mota
- Bayanai da suka fito sun tabbtar wa Legit cewa ana cigaba da bincike da kuma ƙoƙarin kama sauran abokan aikinsa da suka tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Rundunar sojojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin Operation Safe Haven (OPSH) ta samu nasarar kama wani da ake zargin dillalin makamai ne tare da ƙwato bindigogi da alburusai.
Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne a ƙaramar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai ne a kan yadda aka kama mutumin a cikin wani sako da mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama wanda ake zargin ne a cikin wani shirin sintiri na musamman da sojojin suka gudanar a cikin daren Asabar, 3 ga watan Fabrairun 2025, a kan hanyar Jos zuwa Barkin Ladi.
Yadda aka kama mai safarar makamai
Bayanai daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin da ke aiki a ƙarƙashin shirin Operation Golden Peace, sun kafa shingen binciken gaggawa a kan hanyar Jos–Barkin Ladi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin sun kafa shingen binciken ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare.
A lokacin sintirin, sojojin sun tare wata mota kirar Peugeot 206 mai lambar rajista BLD 322 ST daga jihar Filato. A lokacin da waɗanda ke cikin motar suka hango sojojin, sai suka tsere.
Bayan sojoji sun bi su da gaggawa, dakarun sun kama wani mutum ɗaya da ake zargin dillalin makamai ne ga 'yan bindiga mai suna Joseph Davou, mai shekaru 25.
Makaman da aka kwato a Filato
Binciken da aka yi a cikin motar da suka bari ya kai ga gano wasu makamai da alburusai masu tarin yawa da suka haɗa da:
- Bindiga kirar AK-47 guda ɗaya
- Bindiga kirar K2 Daewoo guda ɗaya
- Alburusai da dama da sauransu
Dukkan waɗannan makaman da alburusan an ƙwato su tare da wanda ake zargin, inda aka mika su zuwa hannun sojoji domin ci gaba da bincike.
Matakin da rundunar soji ta dauka
Rundunar OPSH ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin domin gano tushen makaman da kuma kama sauran abokan aikinsa da suka tsere.
Sanarwar ta ce:
“Mun kama wanda ake zargin tare da makamai da alburusai. A yanzu haka yana hannunmu domin gudanar da bincike.
"Haka zalika, mun fara farautar sauran mutanen da suka tsere,”
An kashe dan daba a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen gari sun kakkarya wani dan daba a jihar Kano wanda hakan ya jawo mutuwarsa.
Legit ta rahoto cewa matashin mai suna Aminu Yusuf ya kasance daya daga cikin manyan 'yan daba a unguwar Sheka kuma sun fitini al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng