"Abin da Ka Shuka Shi Za Ka Girba": Za a Rataye Mutum 5 Har Lahira a Jihar Kano

"Abin da Ka Shuka Shi Za Ka Girba": Za a Rataye Mutum 5 Har Lahira a Jihar Kano

  • Kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutum biyar da suka kashe Dahare Abubakar bayan sun zargeta da maita
  • Wadanda ake tuhuma sun bi matar zuwa gonarta a garin Dadin Kowa da ke yankin Wudil, suka daba mata wuka har ta mutu ranar 15 ga Nuwamba, 2023.
  • Kotun ta wanke Nabi’a Ibrahim ta shida da aka tuhume, saboda an tabbatar da cewa ba ta wurin da lamarin ya faru ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Wata babbar kotu a Jihar Kano ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama su da laifin kashe wata mata, Ɗahare Abubakar mai shekaru 67.

Kotun ta umarci a rataye waɗanda ake tuhuma su biyar bisa kashe dattijuwar matar wacce suka kira da mayya kafin su caccaka mata wuƙa har lahira.

Kara karanta wannan

'Hukuncin da ya kamaci masu cin hanci': Inji yaron Buhari duk da zargin rashawa a lokacinsu

Taswirar Kano.
Babbar kotun Kano ta yankewa mutum 5 hukuncin kisa ta hanyar rataya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daily Trust ta ce mutanen da aka yankewa hukuncin sun hada da Da’luta Ibrahim, Abdul'aziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu, da Ayuba Abdulrahman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yanke masu hukuncin rataya a Kano

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Usman Na’abba ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji masu karfi da suka tabbatar da laifin mutanen.

A cewarsa, wannan ya sa ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kotu ta kama su da laifin kisan kai.

"Na yanke wa waɗanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin kisan kai.
"Sannan na wanke Nabi’a Ibrahim, wacce ita ce mutum na shida da ake tuhuma, saboda ba a tabbatar da kasancewarta a wurin da lamarin ya faru ba,” in ji alkalin kotun.

Yadda shari'ar ta faru tun farko

Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Abba Soron-dinki, ya shaida wa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun aikata laifin ne a ranar 15 ga Nuwamba, 2023, a garin Dadin Kowa, ƙaramar hukumar Wudil a Kano.

Kara karanta wannan

Tsige sarki ya bar baya da kura, Gwamna ya daukaka kara bayan hukuncin kotu

"Da misalin karfe 8:30 na safe, wadanda ake tuhuma suƙa hada baki bayan sun zargi Dahare Abubakar da maita, suka rutsa ta a gona suka caccaka mata wuta har ta mutu.."

Ya ce duk da koƙarin da aka yi hanzarta kai ta asibitin ƙaramar hukumar Wudil, liƙita ya tabbatar da rasuwarta.

Shaidun da aka gabatar a gaban kotu

Masu kara sun gabatar da shaidu hudu da kuma hujjoji biyu, ciki har da bayanan da wadanda ake tuhuma suka bayar kafin shari’a da rahoton likitan da ya tabbatar da mutuwar matar.

Sai dai duk da haka, wadanda ake tuhuma sun musanta aikata laifin a gaban kotu, kamar yadda Punch ta kawo.

Masu ƙara sun bayyana cewa laifin da suka aikata ya saba da sashe na 221(a) da sashe na 79 na dokokin Penal Code na jihar Kano na 1991.

Lauyan da ke kare su, Ma’aruf Yakasai, ya gabatar da shaidu takwas, ciki har da wadanda ake tuhuma, domin kare kansu a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Halin da aka shiga bayan an bukaci a sauke sufeton 'yan sandan Najeriya

An rasa rayuka a wurin wuta a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa mutum huɗu sun mutu yayin da rigima ta kaure kan rusau da gwammati ke yi a Rimin Auzinawa, ƙaramar hukuma Ungogo a jihar Kano.

An ruwaito cewa jami'an tsaro ne suka harbe mutanen har lahira a lokacin da mazauna yankin suka nuna adawa da shirin rusa gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel