'Yan Bindiga Sun Bude Wuta ana Rigimar Sarauta, an Harbi 'Yan Sanda 7
- Akalla jami’an ƴan sanda bakwai da wasu mazauna garin Esa-Oke a jihar Osun sun jikkata bayan an bude musu wuta
- An alakanta rikicin da sabani kan nadin sabon sarkin Ido Ajegunle, wanda wasu ke ganin ba ɗan asalin yankin ba ne
- Rundunar ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun tura ƙarin jami’ai domin dakile rikicin da ke ci gaba da tashi a yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Wani rikici mai nasaba da nadin sabon sarki a kauyen Ido Ajegunle da ke ƙarƙashin karamar hukumar Esa-Oke a jihar Osun ya rikide zuwa tashin hankali.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya barke ne yayin da aka bude wuta inda akalla jami’an ƴan sanda bakwai da wasu mazauna yankin suka jikkata.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

Source: Original
Punch ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 3 ga Fabrairun 2025, lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka bude wuta kan ƴan sanda da al’ummar yankin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami’an suna kan hanyarsu ta amsa kiran gaggawa ne lokacin da aka kai musu farmaki.
An farmaki 'yan sanda saboda nadin sarauta
Yemisi Opalola ta bayyana cewa jami’an ƴan sandan suna kan hanyarsu ta zuwa garin Esa-Oke domin amsa kiran gaggawa sai suka ci karo da wani shinge da aka kafa a hanya.
“Jami’an ƴan sanda bakwai ne aka harba, an harbe daya daga cikinsu a wuya. Suna kokarin cire shingen a hanya ne lokacin da wasu suka fara bude musu wuta,”
- Yemisi Opalola
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda suka kai harin sun zo ne cikin wata babbar mota suna sanye da bakaken kaya, suka yi ta harbe-harbe kafin su tsere.
Asalin rikicin sarautar Ido Ajegunle
Rikicin ya samo asali ne bayan gwamnatin jihar Osun ta nada wani masanin fasahar sadarwa daga ƙasar Burtaniya, Timileyin Oluyemi Ajayi, a matsayin sabon sarkin Ido Ajegunle.
Sai dai mazauna garin Esa-Oke sun nuna rashin amincewarsu da nadin, inda suka yi zanga-zangar lumana suna cewa ba za su amince da nada shi da aka yi ba.
An rawaito cewa an fara nuna alamun tashin hankali tun ranar Juma’a bayan zanga-zangar lumana da mazauna yankin suka gudanar, amma lamarin ya kazanta a ranar Litinin.
Martanin mazauna Ido Ajegunle
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin da aka kai yana da nasaba da sabani kan nadin sabon sarkin.
Mutumin ya ce:
“Wadanda suka kai harin suna da alaka da rikicin nadin sarki. Sun bude wuta kan mutane a kusa da ofishin ƴan sandan Esa-Oke”
Haka zalika, bidiyo da aka samu daga mazauna yankin ya nuna mutane biyar da suka jikkata sakamakon harbin bindiga, suna cikin jini a wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun nuna kwarewa, sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
An kama 'yan ta'adda sun hada kai da Sarki
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wasu 'yan bindiga da suke kai hare hare a jihar Taraba.
Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan bindigar sun taso daga jihar Filato ne zuwa Taraba suka kafa sansanin ta'addanci bisa taimakon wani basarake.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
