Sheikh Guruntum Ya Tsage Gaskiya ga Malamai Masu Cudanya da 'Yan Siyasa
- Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya koka kan yadda wasu malaman addinin Musulunci ke mu'amala da 'yan siyasar Najeriya
- Malamin ya yi kira ga malamai da su yi taka-tsantsan da mu’amala da ‘yan siyasa domin kauce wa fadawa tarkon da ka iya rusa da’awarsu
- Ya ce malamai su sani suna da daraja da arzikin ilimi da ya fi dukiya da mulki, kuma su guji fadawa cikin abubuwan da ba su da masaniya a kai
- Wani limamin masallacin Izala a yankin Gadan Dahiru Deba da ke unguwar Pantami a jihar Gombe ya tattauna da Legit kan nasihar Sheikh Guruntum
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, ya fito fili yana bayyana damuwarsa kan alakar malamai da 'yaan siyasa.
Malamin ya yi wannan jawabi ne yayin wani wa’azi da ya gabatar, inda ya yi kira ga malamai da su kasance masu lura da kuma kare martabar da’awarsu daga tasirin ‘yan siyasa.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Guruntum ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya bayyana cewa, duk da cewa akwai ‘yan siyasa nagari, amma akwai masu son amfani da malamai wajen cimma muradunsu.
Kira ga malamai su yi taka-tsantsan
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi kira ga malamai su yi taka tsantsan wajen yin cudanya da 'yan siyasa.
Ya yi nuni da cewa wannan hanya ce da ‘yan siyasa za su iya amfani da ita domin toshe bakin malamai wanda hakan zai iya jawo hana su fadin gaskiya a cikin da’awarsu.
Malamin ya ce 'yan siyasa za su iya shekaru da dama suna kafa tarko domin rusa aikin da’awar malamai saboda jin haushin yadda suke tara jama’a suna karantar da su ilimi.
Ya yi kira ga malamai da su guji shiga cikin al’amuran da ba su da masaniya a kai, domin kauce wa fadawa cikin tarkon da zai iya lalata aikinsu na addini.
Darajar malamai a rayuwar duniya
Sheikh Guruntum ya bayyana cewa malamai suna da arzikin ilimi da ya fi duk wata dukiya ko matsayi a siyasa.
Ya yi nuni da cewa ya kamata malamai su san sun fi 'yan siyasa daraja saboda suna da arzikin ilimi wanda shine ginshikin cigaban al’umma.
A karkashin haka, ya yi kira ga malamai da kar su yarda su kaskantar da kansu a gaban 'yan siyasa saboda abin duniya.
Hukuncin karbar kyautar 'yan siyasa
Malamin ya kuma yi nuni da cewa duk da cewa ya halasta ga malami ya karbi kyauta daga hannun ‘yan siyasa, malamai su kasance masu lura sosai.
Sheikh Guruntum ya ce galibin kyaututtuka na zuwa ne domin a toshe musu baki daga fadin gaskiya ko kuma a matsayin cin hanci.

Kara karanta wannan
'Sun watse mana': Atiku ya fadi abin da yan Najeriya suka yi musu yayin kamfen siyasa
Legit ta tattauna da limamin Izala
Wani limami a masallacin Izala a unguwar Pantami a jihar Gombe ya ce abin da malamin ya fada gaskiya kuma ya kamata malamai su hankalta.
Limamin ya ce:
"Idan da ana samun irinsu suna jan hankalin malamai, da watakila a rage samun cudanyar da ta wuce kima tsakanin malamai da 'yan siyasa.
"Mun ga 'yan siyasa da dama da darajarsu ta zube duk da ana sonsu a da. Saboda haka abu mai sauki ne mutuncin malami ya zube idan ya cudanya da 'yan siyasa."
Babban malamin Izala ya rasu a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala ta sanar da rasuwar mataimakin shugaban malamai na jihar Filato.
Legit ta rahoto cewa shugaban malaman ya rasu ne bayan fama da jinya da ya yi kuma an masa sallar jana'iza a jihar Filato da safiyar ranar Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng