Tsohon Gwamna Ya Hadu da Mutumin da Ya So Kashe Shi a 2006, An Ji Me Ya Fada Masa
- Rauf Aregbesola ya yafe wa Sikiru Olaboye, wanda ya nemi gafararsa bayan an zarge shi da yunƙurin kashe shi a 2006 a Osogbo
- Tsohon gwamnan ya ce bai rike Sikiru ko wadanda suka dauki nauyin harin ba, yayin da ya yiwa mutumin nasiha mai ratsa zuciya
- Aregbesola ya zama gwamnan Osun a 2010 bayan kotu ta soke nasarar Olagunsoye Oyinlola, wanda INEC ta ba nasara a 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ya gana da Sikiru Olaboye, wanda ake zargi da yunƙurin kashe shi a bikin ranar Oroki na 2006.
A ranar Lahadi, Aregbesola ya bayyana cewa ya yafe wa Olaboye, kuma baya da wata ƙiyayya ga waɗanda suka shirya wannan hari.

Asali: Twitter
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan ya ce an faɗa masa cewa Olaboye ya kira wani gidan rediyo a Osogbo domin neman gafararsa.

Kara karanta wannan
'Akwai fa'ida sasantawa da Tinubu': Dan majalisar PDP ya shawarci tsohon gwamna a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aregbesola ya yafewa wanda ya so kashe shi
“A yau, na karɓi Sikiru Olaboye, wanda ya yi yunƙurin kashe ni a bikin Oroki Day na 2006 a Osogbo,” in ji Aregbesola.
Tsohon gwamnan na Osun ya ci gaba da cewa:
“An faɗa mani cewa ya kira gidan rediyo a Osogbo makonnin da suka wuce domin neman gafarata.
“A yau, yayin da nake masa nasiha, na tabbatar masa cewa ban ɗauki wani zafi a zuciyata ba kuma ban nemi ramuwar gayya ba.
“Allah ne kaɗai ke da ikon yin gafara, kuma ina addu’a ya gafarta mana baki daya.”
Harin da aka kai wa Aregbesola a 2006
Rahoton The Cable ya nuna cewa ana gudanar da bikin ranar Oroki a kowace shekara, inda mutanen Osogbo ke taruwa domin ƙarfafa haɗin kai da zumunci.
A ranar 5 ga Agusta, 2006, ‘yan daba da ake zargin magoya bayan Gwamna Olagunsoye Oyinlola ne suka kai wa Aregbesola hari.

Kara karanta wannan
'Munafurcin siyasa ba na irinmu ba ne': El Rufai ya sake ta da kura, ya jaddada matsayarsa
Farmakin ya jawo an lalata aƙalla motoci shida tare da jikkata mutane da dama, a lokacin da zaben gwamna na 2007 ke gabatowa.
Hukumar INEC ta ayyana Oyinlola a matsayin wanda ya lashe zaben, amma kotun daukaka kara ta kwace kujerar tare da ayyana Aregbesola a matsayin gwamna a 2010.
Duba hotunan haduwar Aregbesola da Sikiru a kasa:
Kungiyar Aregbesola ta fice daga APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Omoluabi ta tsohon gwamnan Osun ta fice daga APC gabanin zaɓen gwamna na 2026.
Sakataren kungiyar ya ce rikice-rikicen cikin gida da rashin shugabanci nagari sun raunana APC a jihar Osun.
Rauf Aregbesola ya yaba wa mambobi bisa jajircewarsu, yana mai bayyana amfanin ficewarsu daga jam’iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng