Jerin gwamnoni 9 da kotun koli ta kwace kujerunsu

Jerin gwamnoni 9 da kotun koli ta kwace kujerunsu

Tun daga tushen damokaradiyya a Najeriya ta 1999, kotun koli ta taka rawar gani wajen tabbatar da makomar wasu gwamnoni bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta kammala aikinta.

Duk da cewa kundin tsarin mulkin kasa ne ya ba INEC damar sanar da mai nasara a zabe, kotun koli ce ke da hukuncin karshe don tabbatar da mai nasarar na hakika.

Ga jerin gwamnonin da suka tattara karikitansu daga gidan gwamnati sakamakon hukuncin kotun koli.

1. Celestial Omehia wanda Rotimi Amaechi ya maye gurbi

Omehia ya jagoranci jihar Ribas na watanni biyar kafin kotun koli ta maye gurbinsa da Rotimi Amaechi. Kotun ta bayyana cewa Amaechi ne ya ci zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP amma sai Omehia ya amshe tikitin.

2. Chris Ngige wanda Peter Obi ya maye gurbi

Ngige ya mulki jihar Anambra na shekaru biyu kafin kotun kolin ta bayyana Peter Obi a matsayin halastaccen gwamnan jihar a zaben 2003.

3. Andy Ubah wanda Peter Obi ya maye gurbinsa

Uba na jam’iyyar PDP ya yi kwanaki 17 a kujerar gwamnan jihar Anambra a 2007. Daga nan ne kotun ta kwace kujerar ta mika wa Peter Obi.

4. Oserheimen Osunbor wanda Adams Oshiomhole ya ture

Osunbor na jam’iyyar PDP ya sauka ne bayan watannin 10 da ya dauka a ofishin gwamnan jihar Edo. Adams Oshiomhole ne na tsohuwar jam’iyyar AC ya maye gurbinsa.

5. Olusegun Oni wanda Kayode Fayemi ya maye gurbinsa.

Oni na jam’iyyar PDP ya dauka shekaru biyu a kujerar gwamnan jihar Ekiti kafin kotun kolin ta mika ta ga Kayode Fayemi na jam’iyyar AC a 2010.

Jerin gwamnoni 9 da kotun koli ta kwace kujerunsu
Jerin gwamnoni 9 da kotun koli ta kwace kujerunsu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

6. Olagunsoye Oyinlola wanda Rauf Aregbesola

A 2010, Oyinola na jam’iyyar PDP ya bar kujerar gwamnan jihar bayan da kotun kolin ta bayyana Rauf Aregbesola a matsayin sahihin gwamnan.

7. Mukhtar Idris wanda Bello Matawalle ya maye gurbinsa

Mukhtar Idris ne ya ci zaben jihar Zamfara a 2019 amma an maye gurbinsa da Bello Matawalle bayan da aka gano ba a yi zaben fidda gwani ba a jihar kwata-kwata.

8. Emeka Ihedioha wanda Hope Uzodinma ya maye gurbi

Bayan daukar watanni 8 a ofis, kotun koli ta kwace kujerar Ihedioha a jihar Imo inda ta mika wa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC.

9. David Lyon wanda Duoye Diri ya hankade

David Lyon ne ya yi nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Bayelsa karkashin jam’iyyar APC, amma kuma takardun bogin mataimakinsa ne suka ja aka kwace kujerar inda aka mika ta ga Duoye Diri na jam’iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel