Da dumi-dumi: An fara harbe-harbe a Osogbo, jihar Osun

Da dumi-dumi: An fara harbe-harbe a Osogbo, jihar Osun

Hankalin jama'a ya tashi a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun yayinda aka fara harbe-harbe inda mutane suka fara neman mafaka.

A unguwar Idiya, Ward 8, Unit 1, kuma, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Bayan wannan hari da aka kai Orolu, mazauna garin Disu sunce sun fasa kada kuri'a sakamakon cin mutuncin da akayi musu jiya. Sun bayyana cewa an hanasu fitowa daga gidajensu.

KARANTA WANNAN: Mutanen garin Disu a karamar hukumar Orolu sunce ba za suyi musharaka cikin zaben ba (Bidiyo)

Tun misalin karfe takwas na safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satumba 2018, jami'an hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun isa wurare bakwai da za'a karasa zaben jihar Osun.

Jami'an hukumar yan sanda da sauran jami'an tsaron sun mamaye wuraren domin tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban zaben Olusegun Agbaje ya gargadi wadanda ba kada kuri'a zasuyi ba su nisanci wajen zaben tun yanzu.

Ana gudanar da karashen zaben ne a wurare hudu:

1. Karamar hukumar Osogbo

2. Karamar hukumar Osogbo Ife ta arewa

3. Karamar hukumar Osogbo Ife ta kudu

4. Karamar hukumar Osogbo Orolu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel