Reno Omokri Ya Lissafa Kwasa Kwasai 21 da Ya Kamata Dalibai Su Karanta a Jami'a
- An lissafa Akanta, Noma, Banki da Kudi, Injiniyanci, Likitanci da sauransu a cikin kwasa kwasan da ya kamata a karanta a jami'a
- Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce har yanzu wadannan kwasa kwasan suna da tasiri
- Omokri ya ce akwai jami'o'i da dama ciki har da Oxford da Cambridge da ke rufe wasu kwasa kwasa da suka daina tasiri a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon hadimin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya lissafa wasu kwasa kwasa da ya kamata 'yan Najeriya su karanta a jami'o'i.
Omokri ya ce, wadannan kwasa kwasai 18 da ya lissafa suna da matukar amfani har gobe, musamman duk da zuwan fasahar AI.

Asali: Twitter
Omokri ya lissafa kwasa kwasai 21 masu muhimmanci

Kara karanta wannan
"Na tuba, ba zan kara ba": Kasurgumin dan ta'adda na so gwamnati ta yi masa afuwa
Ya bayyana cewa, amfanin waɗannan kwasa kwasai yana zarce kudi da lokacin da aka bata wajen karantarsu a jami'a daga mahangar nazarin ribar kashe kuɗi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasar ya ambaci lissafi, noma, banki da kudi, injiniyanci, magani da tiyata da sauransu.
Reno Omokri ya lissafa dukkanin kwasa kwasan 18 a shafinsa na X, @renoomokri a ranar Litinin, 18 ga Nuwambar 2024.
Ga kwasa kwasan a kasa:
- Akanta
- Kimiyyar lissafi
- Noma
- Fasahar jikin mutum
- Zanen gidaje
- Banki da Kudi
- Kasuwanci
- Sadarwa
- Tsaro na intanet
- Likitan hakora
- Tattalin arziki
- Ilmin koyarwa
- Injiniyanci (kowane fanni)
- Ilmin ƙasa
- Ilmin kimiyyar duniya
- Tallace-tallace
- Lissafi
- Malamin asibiti (Nas)
- Psychology/Psychiatry
- Kimiyya (Fannonin kimiyya na magani, Physics, da Chemistry)
- Fasaha (Robotics, Aeronautics, IT, AI, da fasahohin zamani)

Kara karanta wannan
Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa
Jami'o'i na rufe kwasa kwasai marasa amfani
Omokri ya ce, jami'o'i da dama suna koyar da kwasa kwasan da suka zama tsohon yayi kuma ba su da alaka da ainihin abubuwan da ke faruwa a yanzu.
“Bisa ga binciken da cibiyar Pew ta gudanar, wasu jami'o'i suna koyar da irin waɗannan kwasa kwasai ne kawai domin ƙara samun kuɗi. Da dama, ciki har da Oxford da Cambridge, suna rufe wasu kwasa kwasan da suka zama tsohon yayi.”
- Reno Omokri.
Kwasa-kwasan da ake yi a jami'ar ABU
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya na koyar da kwasa kwasai masu yawan gaske, daga kimiyya, fasaha, zuwa na ilimi da zamantakewa.
A rahoton Legit Hausa na shekarar 2020, mun lissafa dukkanin kwasa kwasan da ABU ke gudanarwa ciki har da Likitanci, Noma, Lissafa, Lauyanci, Injiniyanci da sauransu.
Asali: Legit.ng