Gwamnati za ta sanya darasin fada a darussan makarantun Najeriya

Gwamnati za ta sanya darasin fada a darussan makarantun Najeriya

Hukumar wasan fada na Kareti, KFN, ta bayyana cewar gwamnati ta fara kokarin ganin an sanya darasin fadan Kareti a tsakanin darussan da ake koyar da dalibai a makarantun Najeriya gabaki daya, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, kuma mataimakin gwamnan jahar Nassarawa, Silas Agara ne ya bayyana haka a yayin taron karkare gasar fadan Kareti da aka shirya a garin Fatakwal na jahar Ribas a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Kurungus! Atiku ya bayyana wanda zai sayar ma kamfanin NNPC idan ya zama shugaban kasa

Gwamnati za ta sanya darasin fada a darussan makarantun Najeriya
Fadan Karate
Asali: Twitter

“Hukumar Kareti ta kammala shirin shigar da fadan Kareti cikin manhajan ilimi na kasa da ake amfani dasu a makarantun Sakandarin Najeriya da ma na manyan makarantun gaba da sakandari.” Inji shugaba Silas Agara.

Mataimakin gwamnan jahar Nassarawa, ya kara da cewa dalilin saka Kareti a cikin manhajar karatun makarantun Najeriya shine domin baiwa daliban damar kare kansu daga dukkanin wani azzalumi da sauran miyagun mutane.

Haka zalika yace darasi akan fadan Kareti zai shirya daliban wajen yanke shawarar shiga aikin Sojan kasa, sojan sama, sojan ruwa, dansanda da ma duk wani aiki daya danganci jarumta da samar da horo mai tsanani.

Daga karshe Agara yace hukumarsu a shirye take ta fafata a wasannin da za’a kara a babbar gasar wasanni ta kasa gaba daya, da sauran manyan gasan wasanni na Afirka da ma na Duniya.

Shi dai shugaban hukumar wasan Kareti na Najeriya Silas Agara an haifeshi ne a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1973, kuma kafin darewarsa mukamin mataimakin gwamnan jahar Nassarawa a shekarar 2015, ya kasance mashawarcin gwamnan jahar, Tanko Almakura akan harkokin wasanni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng