'Na Rasa Budurcina': Bobrisky Ya Fadi Yadda Ya Dirka Wa Budurwa Ciki a Jami'a

'Na Rasa Budurcina': Bobrisky Ya Fadi Yadda Ya Dirka Wa Budurwa Ciki a Jami'a

  • Fitaccen dan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya bayyana yadda ya rasa budurcinsa kuma ya yi wa wata ciki
  • A cewarsa wata Lamide ce ta fara jan hankalinsa har suka kwana tare, bayan wata biyu zuwa uku, ta sanar da shi cewa tana da ciki
  • Bobrisky ya roƙi Lamide da ta nemi mafita, amma ta ƙi, daga baya, ta kai ƙorafi wurin wasu samari da suka tsare shi a cikin ɗaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ikeja, Lagos - Dan daudun nan, Idris Okuneye ya bayyana cewa ya taɓa sa wata mace ta samu juna biyu lokacin yana jami’a.

Dan daudun da aka sani da Bobrisky ya fadi yadda ya rasa budurcinsa bayan haduwa da wata yarinya.

Bobrisky ya koka bayan rasan budurcinsa a Lagos
Dan daudu, Bobrisky ya bayyana yadda aka samu akasi ya yi wa wata ciki. Hoto: @bobrisky222.
Asali: Instagram

Yadda Bobrisky ya rasa budurcinsa a Lagos

Kara karanta wannan

Rikakken dan bindiga ya tuba daga barna bayan sakin wadanda ya kama, ya sauya suna

A wata tattaunawa ta Instagram Live da ya Ogbeni W ya wallafa a shafin X, Bobrisky ya ce lamarin ya faru da wata Lamide lokacin da suke Jami’ar Lagos (UNILAG).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Lamide ce ta fara jan hankalinsa, ta kuma ɗauke masa budurcinsa bayan sun kwana tare.

Bayan wata biyu zuwa uku, Lamide ta zo masa da labari cewa tana da ciki, abin da ya ɗaure masa kai.

A lokacin, Bobrisky yana aji na biyu a jami’a, sai ya roƙe ta da su nemo mafita domin bai shirya ba.

Yadda mace ta yaudari Bobrisky a jami'a

"Da daddare, muna jiran wa zai fara taba wani, ita kuma tana kallona, Ina jin kunya, ban san inda zan fara ba.
"Ta fara shafa ni, muka aikata hakan kuma wannan ne karo na farko kuma na ƙarshe da na yi wani abu da mace.
"Ba a jima da hakan ba, wata biyu ko uku ne kacal, ran nan ma ranar Valentine ce, Ta sayo min rigar ciki da wasu littattafai da nake buƙata a makaranta.

Kara karanta wannan

"Na tuba, ba zan kara ba": Kasurgumin dan ta'adda na so gwamnati ta yi masa afuwa

"Sai ta ce 'Bob, ina da ciki'. Na ce 'ciki yaya? Yaya kika yi? Ni ƙaramin yaro ne fa, na shiga aji biyu yanzu. Kar ki rusa mani rayuwa'."

- Bobrisky

Yadda budurwar Bobrisky ta saka shi a matsala

Daga ƙarshe, Bobrisky ya ce Lamide ta ƙi zubar da cikin, har ta kai ƙorafi wurin wasu samari inda su ka tsare shi.

Ya ce ta nace cewa za ta haifi jaririn, ta fara zagina, ni ma na mayar, sai ta kai ƙorafi wurin wani yaro.

Dokar jinsi: Bobrisky ya yi martanin ga Trump

Kun ji cewa fitaccen dan daudu Idris Okuneye, watau Bobrisky, ya mayar da martani ga dokar sabon shugaban Amurka, Donald Trump kan jinsi.

Dan daudun ya bayyana cewa ya tabbata mace ce shi kuma zai gabatar da shaidar da ta tabbatar da hakan idan an bukata.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan dokar da ke amincewa da nau’in jinsi biyu kawai— namiji da mace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel