Harin Jirgin Abuja zuwa Kaduna: Kotu Ta Samu Muhimman Bayanai a kan Tukur Mamu

Harin Jirgin Abuja zuwa Kaduna: Kotu Ta Samu Muhimman Bayanai a kan Tukur Mamu

  • Wani shaida ya bayyana cewa mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa suna cikin fasinjojin da ‘yan ta’adda suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna
  • An zargi Tukur Mamu da karɓar $120,000 don taimaka wa ‘yan Boko Haram wajen karɓar kuɗin fansa daga iyalan wadanda aka cafke
  • Mamu ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, duk da cewa shaidar ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun daina kula su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Wani shaida da aka sakaya sunansa a matsayin ya gabatar da bayani a shari’ar da ake yi wa Tukur Mamu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

An jagoranci shaidar ne a ranar Alhamis ta hannun lauya David Kaswe, wanda ke wakiltar Antoni Janar na Tarayya (AGF).

Kara karanta wannan

'Ban son belin': Sowore ya buga da 'yan sanda, ya ce ya fi Tinubu karfin iko a baya

Tukur
An ci gaba da shari'ar Tukur Mamu Hoto: MadukaOgwueleka
Asali: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa Mamu na fuskantar shari’a bisa tuhume-tuhume 10 da suka shafi zargin ta’addanci, inda ake zarginsa da taimaka wa ‘yan ta’adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da ake yi wa Tukur Mamu

Jaridar Vanguard ta wa wallafa cewa ana zargin Tukur Mamu da karɓar $120,000 daga hannun ‘yan uwa da ke kokarin ceto ‘yan uwansu da ‘yan Boko Haram suka sace a hanyar Abuja-Kaduna.

Haka kuma, ana tuhumarsa da yin mu’amala da wani Baba Adamu, wanda ake zargin kakakin ‘yan ta’addan Boko Haram ne, ta hanyar musayar saƙonnin murya da suka shafi batun fursunonin da aka sace.

An fara karbar shaida a kan Tukur Mamu

A shaidarsa, wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa an shaida masa cewa mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa suna cikin fasinjojin da suka hau jirgin da ‘yan ta’adda suka kai wa hari a watan Maris na 2022.

A cewarsa, bayan harin, sai ya garzaya zuwa asibitin Kaduna inda aka kwantar da waɗanda suka jikkata, amma bai gansu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Bayan makonni biyu, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya kira shi ta waya, inda ya ba shi damar yin magana da ‘yar uwarsa da aka yi garkuwa da ita.

Shaidar ya ce ya shafe kusan makonni biyu yana tattaunawa da ‘yan ta’addan kafin su nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 200.

Shaidar ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ba shi sunaye da lambobin waya na wasu ‘yan jarida hudu da za a iya tuntuɓa domin tattaunawa.

A cewarsa, daga cikin ‘yan jaridan huɗu, Tukur Mamu ne kaɗai ya amince da daukar nauyin shiga tsakani.

Shaidar ya ce yayin da yake kokarin tara kudin fansa, ya samu kira daga tsohon hafsan tsaron kasa, Lucky Irabor, da kuma tsohon darakta janar na DSS, Yusuf Bichi.

Sojoji sun shiga maganar Tukur Mamu

Shaidar ya ce tsohon hafsan tsaron kasa, Lucky Irabor, ya umarce shi da ya sanar da shi duk abin da ya tattauna da Tukur Mamu.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

A cewarsa, tsohon hafsan ya hada shi da wani kwamitin gwamnati da aka kafa domin sakin fursunonin da aka sace.

Shaidar ya bayyana cewa da zarar ‘yan ta’addan sun tuntubi Tukur Mamu, sai suka daina magana da shi.

“Mun je wurin Mamu, sai ya shaida mana cewa an bukaci mu biya N100 miliyan kowanne."

Mamu ya zargi wasu da zama 'infoma'

Shaidar ya kara da cewa wata rana, ‘yar uwarsa da ke hannun ‘yan ta’addan ta kira shi daga cikin daji tare da ba shi shawarar ya koma ga Mamu domin tattaunawa.

A karshe, shaidar ya ce daga bisani, ‘yan ta’addan sun daina magana da kwamitin CDS, kuma Tukur Mamu ya zarge shi da kasancewa wakilin gwamnati, don haka bai taba son yin magana da shi ba.

Tukur Mamu ya dauki zafi

A baya, kun ji cewa, Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald, ya bukaci Ministan Shari’a a Najeriya da ya janye zargin da ake yi masa na daukar nauyin ta’addanci a Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

A cikin wata sanarwa da lauyansa ya fitar ranar 25 ga watan Maris, Mamu ya yi kira ga gwamnati da ta tsame sunansa daga cikin jerin mutanen da ake zargi da ta’addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel