"Na Tuba, ba Zan Kara ba": Kasurgumin Dan Ta'adda Na So Gwamnati Ta Yi Masa Afuwa

"Na Tuba, ba Zan Kara ba": Kasurgumin Dan Ta'adda Na So Gwamnati Ta Yi Masa Afuwa

  • Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya tuba daga satar mutane kuma ya nemi sassauci daga gwamnati
  • Lauyan gwamnati ya roki kotu ta sake tuhumar Evans da Joseph Emeka, wadanda ake zargi da kisan wasu mutane biyu a 2013
  • Bayan musanta zargin, Evans ya nemi sassauci ta hanyar yarjejeniyar tuba, inda ya shaida wa kotu cewa ya samu shirya daga coci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya shaidawa kotun Jihar Legas a ranar Alhamis cewa ya tuba daga aikata laifuffuka.

Evans, wanda ya bayyana wannan ta bakin lauyansa, Emefo Etudo, ya yi wannan bayanin bayan yarjejeniyar amsa laifin kan zarge-zargen kisan kai da satar mutane.

Dan ta'adda, Evans ya shaidawa kotu cewa ya tuba daga sata da kashe mutane
Mai garkuwa da mutane, Evans ya roki gwamnatin Legas ta yi masa afuwa kan kisan mutane 2. Hoto: High Court
Asali: UGC

Dan ta'adda Evans, ya roki yafiyar gwamnati

Rikakken dan ta'addan ya shaidawa kotun cewa yanzu ya tuba, ya daina satar mutane da kisan kai, kuma ya aika wasika ga gwamanti ta yi masa afuwa, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan gwamnati, Sule Yusuf, ya sanar da kotu cewa za a faro shari’ar daga tushe kuma ya roki kotu ta sake tuhumar wanda ake kara.

Lauyan dan ta'addan watau Evans da lauyan dayan wanda ake ake kara C.N Udeh, basu yi jayayya da wannan bukata ta Sule ba.

Laifuffukan da ake zargin Evans ya aikata

Gwamnati ta zargi Evans da Joseph Emeka da kisan Peter Nweke a ranar 27 ga Agusta, 2013, a layin 3rd Avenue, FESTAC Town da ke jihar Legas.

An kuma zarge su da kisan Chijioke Ngozi, duk a ranar ta 27 ga Agusta, amma Evans da Emeka sun musanta zage-zargen.

Vanguard ta rahoto cewa bayan musanta zargin, lauyan gwamnati, Sule ya roki kotu da ta ci gaba da tsare wadanda ake kara.

Kotu ta sanya ranar fara sabuwar shari'a

Sai dai ya sanar da kotu cewa Evans ya nemi a yi masa sassauci ta hanyar yarjejeniyar amsa laifi, haka shi ma Emeka.

Kara karanta wannan

Barawon da ya sace kayan N500, 000 a masallaci ya shiga hannu

Emefo Etudo ya shaida wa alkaliyar kotun, Adenike Coker cewa duk da sabunta zargin, Evans ya nemi sassauci daga gwamnatin Legas ta hannun ofishin lauyan jiha.

Bayan jawabin lauyan, Alkaliya Adenike Coker ta dage shari’ar zuwa 20 ga Maris, 2025, don yiwuwar fara shari’ar daga farko.

Bayan fitowa daga kotu, Etudo ya shaida wa manema labarai cewa wanda yake karewa ya canza dabi'unsa kuma yana kiyaye koyarwar Cocin Redeemed da gwamnatin tarayya.

"Evans bai nuna alamar nadama ba" - Kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta yankewa mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans hukuncin daurin rai da rai.

Alkaliyar kotun, Hakeem Oshodi ta babbar kotun Ikeja bayan yanke wa Evans hukunci ta ce wadanda ake zargi ba su nuna nadama ba duk da tarin hujjojin da aka gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel