Harshen damo: Shararen mai garkuwa da mutane Evans ya musanta tuhumar da ake masa
- Ya musanta tuhumar ne alhali a baya ya amsa tuhumar
- Lauya mai kare shi ya nemi a daga shari'ar zuwa wani lokaci
- Alkali mai sharia O.H. Oshodi na kotun ya daga shari'ar zuwa 3 ga watan Nuwamba
A yau ne Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, Gawurtaccen mai yin garkuwa da mutane da aka fi sani da Evans ya musanta tuhumar da ake masa a yayin da shari'ar ta sa ta cigaba a babban kotun Ikeja na Jihar Legas.
Shi da sauran mutum 5 da ake zargi, wanda 1 daga cikin su mace ce, duk sun musanta tuhumar a gaban Alkali mai shari'a O.H. Oshodi bayan an yi kwaskwarima ga tuhumar da ake masu, alhali a wancan zaman shari'ar da a ka yi sun amsa tuhumar.
Daga nan ne Lauya mai kare wadanda ake tuhumar ya roki alkalin da ya daga shari'ar. Alkalin kuwa ya amsa rokon na sa ya daga shari'ar zuwa 3 ga watan Nuwamba.
DUBA WANNAN: Yankin Quebec na Kasar Canada ta hana sanya nikabi
Legit.ng ta na harabar kotun a inda ta shaida yadda aka tsananta matakan tsaro saboda wannan shari'ar. Legit.ng kuma ta kawo maku yadda aka gurfanar da shi Evans din da sauran wadanda ake zargi a wannan kotun.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng