Tirkashi: Saurayi da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure a Kano, Hisbah Ta Cafke Su

Tirkashi: Saurayi da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure a Kano, Hisbah Ta Cafke Su

  • Hukumar Hisbah ta kai samame wani gidan cin abinci a Kano, inda ta kama saurayi da budurwa da suka daurawa kansu aure
  • Hisbah ta shaida cewa saurayi da budurwar sun daura auren ne ba tare da izinin iyayensu ba, don haka dole ne ta dauki mataki a kai
  • Mataimakin kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya ce an fara farautar wadanda suka halarci daurin auren

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano karkashin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta kai samame wani gidan cin abinci da ke titin gandun dabbobi (Zoo road).

A yayin wannan samamen, jami'an hukumar sun cafke wani saurayi da budurwarsa da suka daurawa kansu aure a gidan cin abincin mai suna Bababa Restaurant.

Hukumar Hisbah ta yi magana da ta kama saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure a Kano
Hisbah ta cafke saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure a Kano. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Saurayi da budurwa sun daurawa kansu aure

Kara karanta wannan

Hisbah: An kama 'yan 'daɗi soyayya' da suka yi aure a wurin shakatawa a Kano

Mataimakin babban kwamandan ayyuka na hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar ya tabbatar da kama saurayi da budurwar ga jaridar The Punch a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Mujahideen Abubakar ya shaida cewa jami'an hukumar Hisbah sun kai samame gidan cin abincin bayan samun kwarmato a daren ranar Laraba.

"Abin takaici ne a ce saurayi da budurwa su daurawa kansu aure a gidan cin abinci ba tare da sanin iyayensu ba, kawai sai wasu tarin abokai da kawaye."

- Dakta Mujahideen Abubakar.

Mataimakin kwamandan ya shaida cewa hukumar ba za ta zura idanuwa tana kallon ire-iren wadannan abubuwa suna faruwa a jihar Kano ba.

Kano: Hisbah ta kama saurayi da budurwar

A yayin da Dakta Mujahideen ya sanar da cewa an cafke saurayi da budurwar, ya ce yanzu haka ana neman abokan da suka shaida daura auren.

"Tuni hukumar ta fara farautar dukkanin wadanda suka hakarci wannan daura auren da aka yi shi ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta ba da mamaki a Kwara, ta fita a mota ta tattauna da dalibai

"Mun riga mun kama ma'auratan.Yanzu muna farautar abokan angon da suka tsere daga gidan cin abincin bayan jami'an sun kai samame."

Dakta Mujahideen ya ce ma'auratan sun saba dukkanin wasu ladubban daura aure, wanda ya sabawa kundin tsarin shari'ar Musulunci.

Hisbah ta wajabta yin kwas kafin aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah ta ce dole ne masoya su halarci kwas kan zaman aure kafin a daura musu aure a jihar Kano.

Hakanan, hukumar ta ce sai an musu gwajin lafiya tukunna domin kare yawaitar mace-macen auren da ake samu a jihar da kuam kare yaduwar cututtuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel